Home Siyasa Kuncin Rayuwa: Majalisar Wakilai Ta Yi Wa Yan Najeriya Albishir Na...

Kuncin Rayuwa: Majalisar Wakilai Ta Yi Wa Yan Najeriya Albishir Na Sauki Ku Sa

180
0
20240208 175743

Majalisar Wakilai ta yiwa yan Najeriya albishir cewa nan da dan lokaci kadan matsin tattalin arziki da  ake fama da shi zai zama tarihi. In da

ta bawa jama’a hakuri kan tsananin kuncin rayuwa da  su ke fama da shi.

Shugaban Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas ne ya yi wannan albishir jimkadan da kammala taron  Yan jaridu na Duniya a wata hira ta musamman a gidan sa da ke Abuja.

Ko da yake bai fadi takamaman lokacin da za a fara shimfida tabarmar saukin ba, Tajudeen ya ce za a dauki mataki nan ba da dadewa ba, domin bukatar yin haka ta taso.

Kakakin Majalisar Wakilan ya jaddada cewa, Majalisa za ta cigaba da daukar matakai kan batutuwan da suka jibanci yalwar abinci da kuma sha’anin tsaro yadda manoma za su iya komawa harkar noma kamar yadda aka saba.

Abbas ya ce lokaci yayi da Majalisar za ta fara hukunta manyan jamia’n tsaron da suka kasa iya rike amana ta kasa

Ya ce Majalisar na sane da kalubalen tattalin arziki da ‘yan kasa ke fama da shi, kuma tuni su ka fara daukar matakai a wannan fanin inda ya ce sun himmatu wajen shawo kan koma bayan tattalin da mayar da kasar kan turbar cigaba mai dorewa.

Tajudeen ya ce batun karancin abinci da ake fama da shi yana zuciyar sa domin samar da abinci shi ne abu mai muhimmanci ganin cewa rashin abinci yana da alaka da harkar tsaro.

Kakakin Majalisar ya ce Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya bada umurnin a fito da hatsi iri daban daban har ton dubu 42,000 na masara, gero da sauran kayan masarufi a cikin tsare tsare don magance tashin farashin kayan abinci a kasar.

Har ila yau ya ce, klirkiro taro  don nemam shawara da ga na daga matalai  don lalubo mafita ta hamayar yin  tambayoyi ga jama’an da su ke da alhaki don  tambayar su a mamaimakon jama’a.

Ya ce Gwamnati na sane da abubuwa da su ke faruwa kuma ta na daukar matakai na saukar da farashi na kayan abinci sabo da irin tsare-tsare da  ake fitowa da shi.

Mafiyawancin wadan da suke Majalisar zartarwa daga Majalisar Taraiya suke sabo da haka akwai fahimtar ju na  tsakanin su hakan zai taimaka wajen lalubo mafita cikin sauki.

Abbas  ya ce Majalisar za ta saka idon na ganin cewa duk kudade da  aka ware domin aikin jama’a an aiwatar da shi kamar yadda ya kamata domin akwai hukumomi da aka tanada da sai sun tamabatar an aowatar da  aika ce aikace da aka ce za a yi. Idan kama ba a yi ba a kwai hukunce-hukunce da a ka tanada don zartar da hukun

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here