Home Kwadago Kudurin Doka Akan Yan Aikatau Da Masu Daukar Su Aiki Ya Shallake...

Kudurin Doka Akan Yan Aikatau Da Masu Daukar Su Aiki Ya Shallake Karatu Na Biyu A Majalisar Dattawa

110
0
Sen. Hussaini

Majalisar Dattawa ta amincewa Kudurin nan na Doka akan masu yin Aikatau a gidajen masu hali ya shallake Karatu na biyu a wani mataki na tattara bayanai akan Yan Aikatau da kare hakkin su da ga cin zarafi da ga wadanda su ke daukar ta su aiki.

Wannan Kuduri ya  fara shallake karatu na farko ne a Majalisar Dattawa ranar 23 ga Watan Nuwamba na Shekara ta 2023; wanda Dan Majalisar Dattawa daga Jihar Jigawa, Sanata Babangida Hussaini ya gabatar a zauren Majalisar.

Ya ce ya gabatar da wannan Kuduri ne bayan ya yi nazari mai zurfi akan abubuwan da su ke faruwa a Kasarnan shekara da shekaru akan dangantakar da ta ke tsakanin wadanda ake dauka aikatau da su kan su wadanda su ke daukar su aiki a Najeriya.

In da ya kara da cewa abubuwa da dama su  a faruwa ga Yan Aikatau na cin zarafi ta hanyar muzguna mu su da azabtar da su kamar bayi kai wani lokacin ma harda yin lalata da su da ga wadanda su ka dauke su aiki wanda hakan ya sabawa addini da al’ada dama dokoki na kasa-da-kasa na Duniya.

A wani bangaren kuma ya ce su kuma Yan aikatau su ma a na yin amfani  da su wajen samun bayanai na uwayen gidan na su ta yadda akan yi ma su Sata da fashi kai wani lokaci ma akan kashe su a kuma kasa samun bayanai na Yan aikatau da aka hada baki da su.

Sanata Hussaini ya ce burin wannan Kuduri shi ne don ya samo mafita ta hanyar samar da wata hukuma wadda za ta dauki alhakin tattara bayanai akan Yan aikatau wanda ya hada da tarihin su da sanin asalin su da addereshin su kai harma da wadanda za su tsaya mu su a matsayin wakilai ko da ta kwana.

A daya bangaren kuma a dauki matakai na kare mutumcin Yan Aikatau da ga cin zarafi da ga uwayen gidan na su ta hanyar shinfida dokoki da za su kare su da ga cin zarafi kowanne iri ne. Ha ka zalika shi ma wanda ya dauke su aiki za’a adana bayanan sa a wannan Hukuma ta yadda idan wani abu ya faru nan take za’a iya ne mo shi ba tare da wata wahala ba.

Sanata Hussaini ya bayar da misali akan wani abu da ya faru shikaru masu yawa akan wata ma’aikaciyar Nigerian Airways wacce ma su yi mata aiki su ka hada baki aka kashe ta bayan ta dawo daga aiki. Kuma har ya zuwa yanzu ba’a gano inda Yan aikin su ke ba bayan sun gudu.

Ya ce a kwana-kwanannan ma a kafafen sada zumunta wani bidiyo yana yawo na wata Yar aiki ta na azabartar da wani yaro karami da aka bar mata jira. “wadannan kadan ne da ga cikin abubuwan da su ke faruwa da aka sani a Kasarnan” wadan da aka sani dama wadan da ba’a sani ba. Inji shi.

Sanatan ya ce wannan Kuduri wani yunkuri na samar da wata Hukuma karksahin Ma’aikatar Kwadago da kuma tallafin wasu Kungiyoyi na Duniya domin samar da  Dokoki wadanda za su magance matsalar cin zarafi da ake yiwa Yan Aikatau da kuma kare su kan su wadan da ake yiwa aikin da ga kowacce irin barazana da za su iya fuskanta da ga wadan da su ke yi mu su hidima a gidajen su.

Kudurin ya sami goyon baya mai yawa da ga Yan Majalisar Dattawa in da su ka bayar da gudunmawa na goyon bayan samar da wannan Hukuma  da za ta kula da wannan bangare. Abun da ya rage shine, a karatu na uku nan da sati hudu za’a ji ra’ayin Jama’a in da suma za su bayar da gudunmawar su na yadda za a gudanar da Hukumar da samar da Dokoki da za su jagoranci tafiyar da ita a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here