Home Siyasa Kotun kolin Najeriya za ta yanke hukunci kan zaben gwamnan Osun

Kotun kolin Najeriya za ta yanke hukunci kan zaben gwamnan Osun

158
0

A ranar Talatar nan ne 09 ga watan Mayu 2023 Kotun Koli a Najeriya za ta yanke hukunci kan karar da ke kalubalantar zaben Sanata Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP  a matsayin gwamnan jihar Osun.

Tsohon gwamnan jihar Gboyega Oyetola na jam’iyyar APC ne ya shigar da kara a gaban kotu tun da farko.

A shari’ar da ta gabata, wata kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar ta yanke.

Tun da farko hukuncin kotun sauraron koke-koken zabe ya bai wa Oyetola na APC nasara amma ita kuwa kotun daukaka kara sai ta ayyana Adeleke na PDP a matsayin wanda ya lashe zabe a hukuncinta.

Hukuncin da Kotun Kolin za ta yanke a wannan karon shi ne zai raba gardama, a tsakanin mutanen biyu, domin shi ne zai kasance na karshe.

Kwamitin alkalai biyar ne karkashin jagorancin mai shari’a John Inyang Okoro zai yanke hukuncin.

A ranar 16 ga watan Yulin shekarar 2022 ne aka gudanar da zaben gwamna a jihar ta Osun inda hukumar zabe ta Najeriya INEC ta ayyana Ademola Adeleke na jam’iyar PDP a matsayin wanda ya samu nasara.

INEC din ta ce Adeleken ya samu kuri’a 403,371.

Shi kuwa Gboyega Oyetola na jam’iyyar APC ya samu kuri’a 375,27 a cewar hukumar zaben ta INEC.

Hukuncin na ranar Talata shi ne zai tabbatar da sahihin zababben gwamna a jihar ta Osun da ke yankin kudu maso yammacin Najeriya (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here