Home Siyasa Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar wa Adeleke na PDP nasarar gwamnan Osun

Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar wa Adeleke na PDP nasarar gwamnan Osun

169
0

Kotun daukaka kara a Najeriya ta tabbatar da Sanata Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya yi nasara a zaben gwamnan jihar Osun na ranar 16 ga watan Yuli 2022.

Da wannan hukuncin kotun wadda ta zauna a Abuja ta soke hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamna ta jihar ta yi, wadda ta zartar da cewa ba shi ne ya yi nasara ba, abokin hamayyarsa na APC Gboyega Oyetola ne ya ci zaben.

A hukuncin da kotun ta farko ta yi, ta zartar da cewa dan takarar na PDP ba shi ne ya samu mafi rinjayen kuri’u ba, saboda haka ta umarci hukumar zabe ta karbe takardar shedar zaben da ta bai wa Adeleke, ta mika wa Oyetola.

To sai dai a wannan hukuncin na kotun daukaka karar, wanda alkalan kotun uku bisa jagorancin mai shari’a Mohammaed Shu’aibu duka bakinsu ya zo daya, ta soke wancan hukuncin kotun sauraron kararrakin gwamnan, inda ta ce

Kotun daukaka karar ta ce kotun ta baya ba ta yi daidai ba da ta ce an yi aringizon kuri’u, wanda wannan ikirari ne da ta ce kotun ta dogara ne ga shedar da Oyetola da APC suka gabatar, wanda kuma wannan ba abin dogaro ba ne da ya tabbatar da ikirarin nasu.

Alkalin ya ce hakan ba daidai ba ne domin Oyetola da APC sun dogara ne ga bayanan da suke cikin na’ura ba tare da sun duba ainahin rijistar masu zabe ba, wadda ita ce dukkanin ainahin al’amuran zaben suka dogara da ita.

Saboda haka ba su da wata shaida da za ta tabbatar da zargin da suke yi na aringizon kuri’u.

Dangane da batun hurumin kotun daukaka karar na sauraron shari’ar, a nan ma ta zartar da hukuncin da ya yi wa Adeleke dadi, inda ta zartar da cewa bisa sashe na 285(8) na tsarin mulkin Najeriya, tana da dukkanin dama ta sauraron karar da aka daukaka.

Haka kuma kotun ta umarci dan takarar na APC Gboyega Oyetola da jam’iyyar tasa su biya tarar naira dubu 500 kan ɓata wa kotu lokaci.

Tun ainahi a zaben da aka yi hukumar zabe ta Najeriya ta bayyana Sanata Adeleke na PDP a matsayin wanda ya yi nasara a zaben, inda ya kayar da abokin hamayyarsa kuma gwamnan da ke kan kujera Adegboyega Oyetola na APC.

INEC ta sanar da cewa Adeleke ya samu kuri’a 403,371, yayin da Oyetola ya samu kuri’a 375,027.

To amma Oyetola da jam’iyyarsa ta APC sun yi watsi da sakamakon suka garzaya gaban kotu.

A hukuncin da ta yanke ranar 27 ga watan Janairu na 2023 kotun sauraron karar gwamnan karkashin jagorancin mai shari’a Tertse Kume ta soke nasarar Adeleke tare da ayyana Oyetola a matsayin wanda ya yi nasara.

Wannan ne ya sa Sanata Adeleke da PDP suka nufi kotun daukaka kara, wadda ta saurari karar ranar 13 ga watan Maris, amma ta jinkirta hukuncin zuwa ranar juma’a 24 ga watn Maris. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here