Home Kotu da 'Yan sanda Kotu ta fara zaman bayyana hukuncin zaɓen shugaban Najeriya

Kotu ta fara zaman bayyana hukuncin zaɓen shugaban Najeriya

266
0
Court of Appeal

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya, ta fara zama don gabatar da hukunci a kan ƙorafe-ƙorafen da wasu ‘yan takara suka shigar mata, bayan zaɓen watan Fabrairun 2023.

Jami’an tsaron da aka jibge tun da sanyin safiya, sun datse titin da ke zuwa harabar kotun ɗaukaka ƙara ta Najeriya, inda ake zaman.

Kotun mai alƙali biyar a Abuja ta shafe watanni tana karɓar bahasi da kuma sauraron muhawara game da ƙorafe-ƙorafen maguɗi da jam’iyyun adawa na PDP da LP suka yi.

Tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu ne ya lashe zaɓen Najeriya, inda ya samu yawan ƙuri’un da suka kai kashi 37 cikin 100 a zaɓen ranar 25 watan Fabrairu. Abin da ya ba shi galaba a kan Atiku Abubakar na PDP da kuma Peter Obi na jam’iyyar LP.

Wannan, ba shi ne hukuncin ƙarshe da mai yiwuwa za a iya samu game da zaɓen ba, masana shari’a na cewa jam’iyyu na iya ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli wadda za ta yanke hukunci na ƙarshe.

An ga manyan jami’an gwamnatin Najeriya ciki har da mataimakin shugaban ƙasar, Kashim Shettima da shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje da gwamnonin jam’iyyar, duk sun hallara a kotun.

Haka zalika, akwai wasu gwamnonin adawa kamar na jihar Bauchi, Bala Mohammed a kotun da shugaban PDP, Umar Iliya Damagum.

Mai shari’a Haruna Tsammani tare da sauran alƙalan kotun sun fito inda suka zauna don fara gabatar da hukunci.

Livy Uzogwu shi ne wanda ke jagorantar lauyoyin jam’iyar LP, inda ya gabatar da kansa.

Tribunal a

An fara da kiran ƙarar jam’iyyar APM

Za a fara da shari’ar jam’iyyar APM da ta shigar kan Bola Ahmed Tinubu da Hukumar Zaɓe ta INEC da Kabiru Masari.

Sai dai an shaida wa kotun cewa masu ƙarar ba su hallara ba.

Mai shari’a Tsammani zai farada karanto hukncin kotu game da ƙarar jam’iyyar APM

Ƙarar Atiku

Akawun kotu ya ci gaba inda ya kira ƙarar da Atiku Abubakar na PDP ya shigar da waɗanda ake ƙara.

Barista Chris Uche ne ke wakiltar masu ƙara na ɓangaren Atiku Abubakar.

Ya fara gabatar da dalilai da suka nuna cewa mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima bai cancanta ya tsaya takara ba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here