Home Siyasa Kogi: Manyan ƴan takaran da za su fafata a zaɓen gwamnan jihar

Kogi: Manyan ƴan takaran da za su fafata a zaɓen gwamnan jihar

133
0
Kogi Yan takarar Gwamna

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) ta ce ta shirya tsaf domin gudanar da zaɓen gwamna a jihohin Kogi da Imo da kuma Bayelsa.

Za a gudanar da zaɓukan jihohin ne a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamban 2023.

A tsawon watanni bakwai da suka wuce, ƴan takarar gwamna a jihar Kogi, na ta gudanar da yaƙin neman zaɓe a ƙoƙarinsu na ganin sun kai ga nasara.

Yanzu haka akwai ƴan takara 18 da ke takarar gwamnan a jihar ta Kogi.

Ƴan takarar za su fafata ne domin ganin wanda zai maye gurbin gwamna Yahaya Bello mai barin gado, wanda ke kammala wa’adin mulkinsa karo na biyu.

Jam’iyyar APC mai mulkin jihar na yin duk mai yiwuwa wajen ganin ta riƙe kujerar gwamnan yayin da jam’iyyun adawa kuma ke ƙoƙarin ganin sun kwace mulki daga hannun APCn da ke kan mulki tsawon shekara takwas.

Cikin jam’iyyu 18 da INEC ta tantance domin shiga zaɓen gwamna a jihar Kogi ya zuwa ranar 9 ga watan Nuwamban, 2023, ana ganin cewa shida ne kawai ke a kan gaba gabanin zaɓen na ranar Asabar.

Masana harkokin siyasa a jihar na ganin cewa fafatawar za ta fi zafi ne tsakanin jam’iyyu uku, APC, PDP, da kuma SDP.

Masanan sun ƙara da cewa manyan ƴan takarar uku da ke sahun gaba a zaɓen sun fito ne daga kabilu daban-daban, kamar Ebira, Igala, da kuma Okun, kuma hakan zai iya yin tasiri sosai kan sakamakon zaɓen.

Sun ce yayin da jam’iyyar APC za ta iya samun yawan kuri’u daga tsakiyar jihar, SDP kuma za ta iya bayar da mamaki a gabashin jihar, inda ita kuma PDP mai ɗimbin magoya baya a yammacin jihar, za su zaɓi Dino Melaye.

Manyan ƴan takarar guda uku da ake ganin fafatawar za ta fi zafi tsakaninsu su ne:

Sanata Dino Melaye – PDP

Sanata Dino Melaye shi ne mutumin da zai yi wa jam’iyyar PDP takara a zaɓen gwamnan Kogi da ke tafe.

An haife shi ne a watan Janairun 1974 kuma ɗan siyasa ne mai yawan haifar da ce-ce-ku-ce.

Tsohon ɗan majalisar dattawan, ya yi karatun sakandare a Kwalejin Abdulaziz Attah, da ke Okene.

Daga nan ya tafi Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarar 2000 inda ya karanta ilimin Geography.

A shekara ta 2021, ya kammala karatu a Jami’ar Baze, inda ya karanta fannin Shari’a.

Melaye ya wakilci mazaɓar Kogi ta Yamma a majalisar dattijan Najeriya daga 2015-2019.

Zamantowarsa dan takarar jam’iyyar PDP, ya ƙara iza wutar adawa tsakaninsa da jam’iyyar APC a jihar.

Ana kuma ganin cewa ɗimbin magoya bayan jam’iyyar PDP na tare da shi, kuma suna shirye domin zaɓen shi a matsayin gwamnan jihar Kogi.

Ododo Ahmed Usman – APC

Ododo Usman shi ne ɗan takarar zaɓen gwamnan jihar Kogi a karkashin jam’iyyar APC a zaɓen na ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.

Usman-Ododo wanda ɗan ƙabilar Ebira ne da ya fito daga garin Okene, ya yi digirinsa na farko a fannin Akanta a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Ya kuma yi digirinsa na biyu a fannin kasuwanci a Jami’ar Legas.

Kafin samun zama ɗan takarar gwamna a jam’iyyar APC, ya kasance Babban mai binciken kuɗi na ƙananan hukumomi na jihar, tsawon shekara bakwai da rabi, kuma an yi imanin cewa ya taka rawar gani a gwamnatin Yahaya Bello.

Murtala Yakubu Ajaka – SDP

Murtala Yakubu Ajaka ya kasance babban jigo a jam’iyyar APC a jihar Kogi, kafin komawarsa SDP.

Mista Ajaka ya fito ne daga karamar hukumar Igalamela, da ke gabashin jihar Kogi. Mazaɓar tana da yawan masu kaɗa kuri’a.

Ya koma jam’iyyar SDP ne bayan kasa samun tikiti a APC, inda daga bisani ya samu nasarar zama ɗan takarar SDP a zaɓen gwamnan Kogi na 2023.

An yi imanin cewa ɗan takarar na SDP watakila zai samu kuri’u masu yawa a gabashin Kogi.(BBC).

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here