Home Siyasa Ko gezau don wasu sun fice daga jam’iyyarmu — APC

Ko gezau don wasu sun fice daga jam’iyyarmu — APC

193
0

Jam`iyyar APC mai mulki a Najeriya, ta ce ko gezau dangane da ficewar da wasu manyan`ya`yanta ke yi daga jam`iyyar.

APC ta ce sauya-shekar da Hajiya Naja`atu Muhammad, ta yi daga jam`iyyar zuwa PDP duk kuwa da girman kujerarta ta darakta a gangamin yakin neman zabe na dan takarar shugaban kasa na APC wato Bola Tinubu, da kuma ficewar da tsohon gwamnan jihar Adamawa, Senata Bindo Jibrilla, ba su dadarata ga kasa ba, saboda a cewar jam`iyyar da ma can babu abin da suke tsinanawa.

Mallam Mahmud Jega, shi ne mai bai wa dan takarar shugaban kasa na jam`iyyar APC shawara a kan harkar yada labarai, ya kuma shaida wa BBC cewa, Allah ya raka taki gona, domin akwai wadanda idan ma sun fita daga jam’iyya murna ma ake yi.

Ya ce, “ Wadanda suka fice daga APC, dama an tattara za a kore su shi ne da suka ji labari sai suka yi sauri suka fice daga jam’iyyar”.

Mahmud Jega, ya ce ba sa raba daya biyu cewa Naja`atu `yar koren PDP ce, saboda tana sanar da fitar ta daga APC ba ta tsaya wata-wata ko waige-waige ba, sai aka ganta da dan takarar shugaban kasa na jam`iyyar PDP Atiku Abubakar.

To sai dai kuma anata bangaren, babbar jam’iyyar adawa a Najeriyar PDP, ta ce hijirar da Naja`atu da sauran manyan `ya`yan APC ke yi zuwa PDP, babbar nasara ce ga jam`iyyar da kuma dan takararta a wannan lokaci da ake gab da babban zabe, kuma `yan Najeriya sun gaji da fada ba cikawar da APC ke yi.

Mista Daniel Hassan Bwala, daya ne daga cikin masu magana da yawun gangamin yakin neman zaben Atiku Abubakar, ya shaida wa BBC cewa, su wannan hijira da ake zuwa jam’iyyarsu ai karuwa ce, domin mutane sun fara fahimtar gaskiya.

Jam`iyyar PDP dai ta yi ikirarin cewa akwai karin wasu jiga-jigan APC da nan gaba kadan za su tare a wajen ta, wasu kuma za su ci gaba da yi mata aiki a APC.

Amma APC a nata bangaren ta ce zancen kawai PDP take so, wai an ce da gwauro yaya iyali, tana zargin cewa PDP ba ta iya hada kan `ya`yan cikinta ba ma ballantana ta rungumi na wani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here