Home Siyasa Kirkiro Da Yan Sandan Jihohi Tamkar Samar Da Hukumar Barayi Da Yan...

Kirkiro Da Yan Sandan Jihohi Tamkar Samar Da Hukumar Barayi Da Yan Fashi Da Makami Ne A Najeriya – Inji Hon. Fulata

117
0
Hon. Fulata a

An baiyana yunkurin kirkiro da Yan Sandan Jihohi da wasu gwamnoni su ke yi da tamkar wani mataki na samar da hukumar barayi da Yan fashi da makami a maimakon samar da tsaro a kasarnan.

Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar kananan Hukumomin Birniwa daKirikasamma da Guri da ga Jihar Jigawa, Hon. Abubakar Hassan Fulata ne ya yi wannan harsa she a wata hirar sa da Yan Jaridu a ofishin sa da ke Majalisar a birinin Taraiya Abuja a ranar Talata biyo bayan tsallake karatu na biyu da Kudurin ya yi.

Ya ce mafi yawan Gwamnoni ba sa iya biyan ma’akatan da su ke karkashin kulawar su sabo da haka idan aka kara mu su wani nauyi na wasu mutane wadanda za a bawa horo kuma a ba su makamai wanda idan akai hakan kuma a ka kasa ba su albashin su tamkar an ba su dama ne da su tsare hanya su yi fashi da makami.

“ Wasu Jihohi ba sa iya biyan albashin Ma’aikatan su. I dan an dauko wasu mutane an horar da su, an koya mu su harbin bindiga, an ba su bindigogi kuma an kasa biyan su albashi. Ka ga ka kirkiro hukumar barayi da Yan fashi da makami ke nan a jihohi, Wannan zai kawo kalubale babba idan a ka yi wannan”. Inji Shi.

Bayan haka, Hon. Fulata ya kara da cewa kuma a na zargin cewa idan a ka bawa Gwamnonin dama su ka mallaki Yan Sandan karkashin kulawar su a kwai yiwuwar cewa za su iya yin amfani da su wajen cuzgunawa yan adawa a jihohin na su.

Fulata ya ce duk da ya ke kudurin ya wuce karatu na biyu a Majalisar Wakilai kuma shi ne karo na biyar da a ka yi yunkurin kafa Hukumar Yan Sanda ta Jihohohi ya na ganin koda an gabatar da kudurin sau  goma  ba zai wuce ba sabo da sai an sami amincewar biyu bisa uku na Yan Majalisar Wakilai da Yan Majalisar Dattawa da kuma Yan Majalisar Jihohi 36 da ke kasarnan.

A daya bangaren kuma, dan Majalisar ya ce shima yunkurin  da wa su Yan Majalisar su ke yi na mayar da tsarin shugabancin Najeriya da ga tsarin Mulkin Shugaba Mai Cikakken iko wato “ Presidential” Zuwa “Parlimentary” wato tsarin “Prime Minister” shi ma abu ne da ba zai yiwu ba.

Fulata ya ce duk da ya ke tsarin zai kawo sauki na ka she kudaden Gwamnati wajen gudanarwa da ragewa shugaban kasa karfin fada aji da sauran su. Matsalar it ace, tsarin zai haifar da rudani da kabilanci da bangaranci da sauran su.

In da ya yi Karin haske cewa a shekara guda za a iya samun canji na shugaban biyar koma sama da haka sakamakon cewa Yan Majalisa ne suke da ikon na da Firiminista kuma da zarar ya yi wani abu da bai yi mu su ba za su iya cire shi  a nan take kuma su nada wani.

Ya bayar da misali da Ingila da suke da cigaba da kwarewa da kuma bin doka an sami caji na shugabanci sau uku a Majalisar Kasar a cikin shekara guda. Wanda y ace a Najeriya wadda ake da matsaloli na bangaranci da kabilanci da sauran su. A irin wannan kasa, tsarin mulkin Firiminista zai haifar da rudani mai yawa.

Ya ce a kasa irin ta Najeriya da kabilanci da bangaranci da addini ya ke tasiri cire shugaban zai zamo tamkar wasan yara ne kawai sabo da irin rawar da wadannan abubuwa su ke takawa a zamantakewar mu.

Fulata ya ce wannan ra’ayin sa ne amma koma me ne idan Kudurin ya wuce karatu na biyu za a ji ra’ayin jama’a. Wanda a Majalisar Dattawa da ta Wakilai a na bukatar samun amincewa kashi biyu bisa uku na Yan Majalisar. A jihohi ma a na bukatar samun amincewa kaso biyu bisa uku na Jihohi 36 kafin a kai wa Shugaban Kasa ya amince da shi. Wanda ya ce lokaci ne kawai zai tabbatar da yiwuwar sa ko rashin yiwuwar sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here