Home Noma da Kiwo Kasafin Kundi Na 2024: Majalisar Dattawa Ta Bukaci Gwamnatin Tinubu Da Ta...

Kasafin Kundi Na 2024: Majalisar Dattawa Ta Bukaci Gwamnatin Tinubu Da Ta Ware Kaso 10 Ga Harkar Noma

258
0
Sen. Mustapha 2

Majalisar Dattawa ta yi kira na musamman ga Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da ta ware kaso goma na kasafin kudi na shekara ta 2024 ga harkar Noma  a wani mataki na wandata kasa da abinci wanda shi ke samar da kaso 70 na bukatar Yan Najeriya.

Shugaban Kwamitin Nomo na Majalisar Dattawa, Sanata Mustapha Salihu da ga Jihar Neja ne ya yi wannan kira a yayin wani zama na musamman da Majalisar ta shirya da Ministocin Noma da Shugabannin Ma’aikatu na Namo da ke Kasarnan da ya gudana a Majalisar ranar Alhamis.

Sanata Mustapha ya ce idan an bawa Noma kulawar da ya dace za a yaki talauci da yunwa da rashin aikin yi da samun yalwatar arziki tare da magance barazanar tsaro da ta addabi kasarnan.

Sanatan ya kara da cewa kamar yadda ya ke a cikin kudurin Majalisar Dinkin Duniya cewa duk kasar da ta ke so taci gaba to ya zama wajibi ta ware kaso 10 na kasafin kudin ta ga harkar Noma don wadata kasa da abinci.

“tunda aka kirkiri kasarnan tsohon Shugaban Kasa Marigayi Umaru Musa Yar’adua ne ya taba ware kaso 3 na kasafin Kudi na Kasarnan ga harkar Noma; sabo da haka a wannan zamani da ake cikin tsananin talauci da matsi na tattalin arziki akwai bukatar a ware sama da kaso 10 ga harkar Noma” in Sanata Mustapha.

Sanata Mustapha ya ce dalilin shirya taron na masu ruwa da tsaki na Noma na Gwamnatin Taraiya shine domin Majalisar ta ji da ga gare Su irin shirye-shirye da su ke da shi akan harkar Noma domin a samu fahimta tsakanin Majalisar Dattawa da Su a wani mataki na wadata Kasa da abinci domin samun saukin rayuwa.

Yace Majalisar ta ji duk irin tsare-tsare da su ke da shi akan harkar Noma kuma Majalisar za ta yi duk mai yiwuwa wajen hada gwiwa da Fadar Shugaban Kasa domin ganin sun kasance a shafi guda a wani mataki na bawa Noma kulawar da ta dace don samar da abinci wadatacce wanda idan an yi hakan tabbas za a samu saukin rayuwa a kasarnan.

A na sa bangaren, Karamin Ministan Noma, Sanata Sabi Abdullahi wanda ya yiwa Yan Jaridu karin haske bayan gama taron ya ce manufar taron shine a samu fahimtar juna tsakanin Fadar Shugaban Kasa da Majalisar Taraiya a wani mataki na inganta harkar Noma wanda shine kashin bayan tattalin arzikin Najeriya.

Sanata Sabi ya kara da cewa a matsayin su na sababbin Ministoci da sababbin Yan Majalisar Taraiya akwai bukatar a sami fahimatar juna domin kauracewa rigingimu da ka iya aukuwa tsakanin Majalisar da Fadar Shugaban Kasa.

Ya ce Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya bawa Noma muhimmanci sabo da haka ne su ke so a sami fahimtar juna don samar da wadaccen abinci wanda hakan zai kawo sauki ga Yan Najeriya musamman a wannan lokaci da ake fama da matsi na tattalin arziki.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here