Home Siyasa Kasafin kudin 2024: Zai Daga Rayuwar Yan Najeriya Inji Tinubu

Kasafin kudin 2024: Zai Daga Rayuwar Yan Najeriya Inji Tinubu

230
0
20231129 114213

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinibu ya gabatar da kasafin Kudi na sama da Nara Tiriliyan 27 a wani zama na hadaka da ya hada Majalisar Datttawa da ta Wakilai a yau Laraba.

Shugaban Majalisar Datttawa Godswill Akpabio ya nuna yadda Majalisar ta shirya don baiwa shugaba Kasa Bola Ahmad Tinubu goyan bayan da ya kamata don cimma burin wannan gwamnati.
Ya ce burin su shine a inganta rayuwar Yan Najeriya a fannoni da tattalin arzikin Yan Najeriya da inganta tsoro da sauran su.
Akpabio ya kara da cewa nasarorin da Tinubu ya samu lokacin da ya na gwamnan Lagos wasu alamu ne na cewa zaiyi amfani da irin kwarewa don inganta Najeriya.
Ya roki gwamnatin Tinubu da ta yi kokari dan rage tarun basuka da suka yiwa kasarnan dabaibayi. Ya ce yin haka zai taimaka wajen inganta rayuwar Yan Najeriya.
Daga karshe ya ce Majalisar Datttawa ta 10 za ta yi duk mai yiwuwa  wajen ganin sun amince da kasafin kudin da ya gabatar. In da ya roki Ministoci da kada su yi tafiya a lokacin da ake amincewa da wannan kasafin kudi.
A jawabin sa Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya roki Yan Majalisar da su bawa Gwamnatin sa hadin kai da goyon baya wajen ganin an samawa Yan Najeriya saukin tattalin arziki.
Ya ce cire Tallafin Mai da gwamnatin sa ta yi an yi shine da kyakkyawan niyya don warware matsalolin da suka addabi kasarnan a maimakon amfanar wasu timaru a kasarnan.
Shugaba Tinubu ya ce wannan kasafin kudi da ya yiwa suna da Kasafin Kudi da zai daga matsayin Yan Najeriya ta hanyar bunkasa rayuwar su.
Ya ce kasafin kudi zai maidan hankali wajen yin hadin gwiwa da Yan kasuwa wajen ganin wajen gudanar da manyan aiyuka a kasarnan.
Tinubu ya  kara da cewa wannan kasafin Kudi zai taimaka wajen inganta rayuwar Yan Najeriya ta hanyar karfafa doka don yin aiyuka da za su kayo cigaba.
Kasafin kudin na Naira Tiriliyan 27.57 wanda aka saka ginshikin sa akan kashe Naira Tiriliyan 8.7 wajen gudanar da manyan aiyuka. Za a kashe Naira Tiriliyan 8.25 wajen biyan bashi .
Bayan haka ana saran hakar danyen Mai ganga miliyan 1.78 a kowacce rana. Ita kuma farashin Dala zai kasance Naira 1 akan Dala 750.
Anasa jawabin, Shugaban Majalisar Wakilai Hon. Tajudeen Abas ya nuna shirin Majalisar na yin aiki tare wajen ganin an sami cigaba a kasarnan.
Abas ya ce za suyi duk mai yiwuwa don ganin sun amince da wannan kasafin kudi cikin kankanin lokaci.
Kakakin Majalisar Wakilai ya roki Shugabannin ma’aikatun gwamnatin Taraiya da su bawa Majalisar hadin kai a yayin amincewa da kasafin kudin da lokacin da za su zagaya don duba aiyukan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here