Home Mulki Ķasafin Kudin 2024: An Yiwa Yan Najeriya Albishir Cewa Gaba Za...

Ķasafin Kudin 2024: An Yiwa Yan Najeriya Albishir Cewa Gaba Za Ta Fi Baya Kyau

130
0
20231129 114213
Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsare, Atiku Bagudu ya yiwa Yan Najeriya albishir cewa Kasafin Kudin da Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya gabatar na dauke da Tsare-tsare da za su inganta rayuwar Yan Najeriya fiye da yadda ake yi a baya.
Ministan ya baiyana haka ne ga Yan jaridu jimkadan bayan da Shugaban Kasa Bola Tinubu ya gabatar da kasafin Kudi a gaban Majalisun Taraiya a Abuja.
Bagudu ya ce Shugaban kasar ya tsara kasafin kudin ta yadda yan Najeriya za su sami sauki na matsin rayuwa sakamakon cire tallafin Man Fetur da aka yi.
Ya ce kasafin kudin ya yi tanadi na saukaka rayuwar Yan Najeriya a fannoni kamar su wadatar da Kasa da abinci da ilimi da lafia da Zirga-zirga da sauran su.
Atiku Bagudu ya kara da cewa Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya na da tausayi da hangen nesa shi ya sa ya fito da Tsare-tsare da za su fidda kasarnan da ga hali na kaka na kayi da ake ciki.
Kasafin kudin wanda aka yiwa lakabi da kasafi da ke cike da buri an gina shine akan kudade da za su rinka shigowa da ga tallafin da aka cire da kuma fadada kudaden shiga da ga ma’adai da za a rinka hakowa.
Ministan Kasafin Kudin ya ce wannan kasafin kudi na sama da Naira Tiriliyan 27 za a samo sama da Naira Tiriliyan 18 da ga karin hanyoyin samun kudaden shiga da gwamnatin da fito da su.
Ya ce wannan zai sa a rage ciyo bashi sannan kuma za a rinka rage bashi da ake bin kasarnan.
Atiku Bagudu da ga karshe ya ce Yan Najeriya sun yi hakuri kuma ya kara rokon su da su kara hakuri domin kuma akwa kyakkyawan fata cewa Kasarnan za ta samu cigaba fiye da yadda ake a baya.
Shima dan Majalisar Datttawa da Jihar Sokoto, Aliyu Wamako ya nuna kwarin gwiwa cewa Kasafin Kudin ya kunshe da tanade-tanade da za su inganta rayuwar Yan Najeriya.
Hon. Alasan Ado Doguwa shima ya nuna gamsuwar sa game da kasafin kudin inda ya yiwa Yan Najeriya albishir cewa za a samu gagaramin cigaba a karkashin jagorancin Bola Ahmad Tinubu.
Dan Majalisar Taraiya da ke Wakilta Faskari da Kankara da ga jihar Katsina, Muhammad Jamil ya gamsu da tsarin Kasafin Kudin kuma ya na da yakini cewa Kasafin Kudin zai inganta rayuwar Yan Najeriya a fannoni da dama.
Hon. Dr. Auwalu Gwalabe da ke Wakiltar al’umar Katagum da ga Jihar Bauchi  ya nuna jin dadin sa da ya kasance da ga cikin wadanda su ka karbi wannan kasafin kudin kuma abin da ya faranta ma sa ran shi ne makudan Kudade da aka ware dan Inganta rayuwar talakawa wadanda su suka fi shan wahala.
Bayan ha ya yaba da yadda aka ware Kudade don tallafawa dalibai ta hanyar ba su bashin Kudade da zai dauki nauyin keratun su. Ya hakan zai tallafa kwarai wajen samar da ilimi a kasarnan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here