Home Siyasa Kare Kasafin Kudi 2024: Zamu Fasa Kwai Idan An Zo Da Rashin...

Kare Kasafin Kudi 2024: Zamu Fasa Kwai Idan An Zo Da Rashin Gaskiya – Sanata Hanga

139
0
Hanga

Majalisar Dattawa ta ce a shirye ta ke ta fasa kwai idan aka zo mata da wani batu da ke dauke da lauje cikin nadi a cikin kasafin kudi na shekara ta 2024 da ake karewa a gabanta a halin yanzu.

Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kano ta tsakiya da ga Jam’iyar NNPP, Sanata Rufai Sani Hanga ne ya fadi haka a hirarsa da Yanjaridu a ofishin sa da ke Majalisar a birinin Taraiya Abuja a ranar Laraba.

Da ya ke karin haske akan sabon tsari da su ka fito da shi wajen kare kasafin kudin ya ce sun yi haka ne domin su sami dama su tantance kasafin kudin cikin kankanin lokaci sabanin yadda su ke yi a baya na  bin hanya mai tsawo.

Ya ce a wannan tsarin na yanzu sun amince da su rinka zama na Hadaka tsakanin shugabannin na Majalisar Dattawa da na Wakilai a guri guda in da za su yiwa kasafin kudin kwaf daya lura da kankanin lokacin da su ke da shi.

Sanata Hanga ya ce a wannan tsari ma’aikatun gwamnatin Taraiya ne za su gabatar da ainahin gundarin kasafin kudin ga Majalisar a yayin da shugaban kasa tuni ya bayar da gajeren rahoton abun da kasafin kudin ya kunsa.

“ a lokacin tantancewa za mu bada muhimmanci ne wajen ganin mai suka yi da kudin da aka basu a baya kuma mai su ke bukata a yanzu. Idan mu ka ga abun da sukayi bai kai abun da su ka ce za su yi ba to sai mu tuhume su. Ta haka za mu gano gaskiyar al’amari. Idan sun yi ba dadai ba sai mu fasa kwai”.

Sanatan ya kara da cewa Majalisa ta 10 ta sha alwashin yin aiki na gaskiya sabanin yadda aka saba yi a baya. “ Mu na tare da ku Yanjarida, idan an yi wani abu na rashin gaskiya za mu kira ku mu fasa kwa. Kun san mu ba zamu yi shiru ba idan an zo da rashin gaskiya.

Da ga karshe ya yi alkawarin cewa Majalisar za ta kammala tantance Kasafin kudin cikin dan kankanin lokacin da aka di ba mata. In da ya yi kira ga Yan Najeriya da su kara hakuri cewa Majalisar a shirye ta ke ta kare bukatun su domin su suka turo su Majalisar don su kare hakkin su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here