Home Uncategorized Kara Kudin Wutar Lantarki: NASSI Ta Nemi Shugaba Tinubu Da Ya Tallafawa...

Kara Kudin Wutar Lantarki: NASSI Ta Nemi Shugaba Tinubu Da Ya Tallafawa Kananan Masana’antu

195
0
IMG 20240419 WA0052

Kungiyar Masu Kananan Masana’antu ta Kasa ( NASSI) ta yi kira ga Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu da ya kawo dauki na musamman ga Kananan Masana’antu sakamakon cire tallafin wutar lantarki.

Shugaban Kungiyar na Kasa Chief Dr. Soloanimon Vongfa ne ya yi wannan kira a taron Yan Jaridu da Kungiyar ta shirya a birnin tarayyar Abuja a yau Juma’a.
Ya ce cire tallafin zai durkusar da Kananan Masana’antu wadanda dama suke cikin wani hali na tabarbarewa sakamakon matsaloli da su ka dabaibaye su.
Chief Vongfa ya ce   wutar ba ta wadaci kamfanonin ba ga Matsalar tashin farashin kayan da su ke sarrafawa da sauran matsaloli ma su yawa.
Shugaban ya ce akwai bukatar Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu da ya fito da wani tsari na tallafawa Kananan Masana’antu domin su ne kashin bayan tattalin arzikin kasarnan.
Vongfa ya kara da cewa Kungiyar ce ke samar da aiyukan yi a kasarnan fiye da kowanne bangare. Bayan haka su suka fi samar da kudaden shiga wanda ke bunkasa tattalin arzikin Yan Najeriya.
NASSI ta bukaci Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da ya shirya wani zama na musamman da masu ruwa da tsaki akan harkar wutar lantarki domin su fahimci wannan tsari na kara kudin wutar lantarki a lokacin da ake fama da hauhawar tashin farashin kayan sarrafawa.
Chief Vongfa ya bukaci Gwamnatin Taraiya da ta fito da karin wasu hanyoyi na samar da wutar lantarki kamar ta hasken rana da iska da sauran su a wani mataki na inganta wutar lantarki a kasarnan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here