Home Siyasa Juyin Mulki A Africa: Ba Zai Yiwu A Najeriya Ba – Inji...

Juyin Mulki A Africa: Ba Zai Yiwu A Najeriya Ba – Inji Hon. Tukura

190
0
Hon. Tukura

Dan Majalisar Taraiya mai Wakiltar Zuru, Fakai, Danko-Wasagu/Sakaba da ga Jihar Kebbi Hon. Kabir Tukura Ibrahim ya baiyana cewa Yan Najeriya su sha kurumin su cewa baza a samu Juyin Mulki a Najeriya ba kamar yadda ake samu a wasu kasashe na Africa.

Ya fadi haka ne a wata hira da an Jaridu da ya gudanar ranar Alhamis a ofishin sa da ke Abuja inda ya ce kasashen da aka yi juyin mulki a Africa kasashene dake karkashin mulkin mallaka na Faransa a sakamakon danniya da kaka nakayi da suka jefa kasashen ciki duk da cewa suna ikirarin sun basu mulkin kai.

Hon. Tukura ya kara da cewa akwai bambamci idan aka lura da irin Yancin da Kasar Birtaniya da Kasar Faransa suka bayar. In da ya ce a irin Yanci na Birtaniya Najeriya ta na gudanar da abubuwa da kanta ba tare da katsa landan da ga kasar Birtaniya ba.

A in da ya ce a irin Yanci na Faransa, kasashen da Faransa ta baiwa Yanci har yanzu ita take tafiyar da kasashen da ta bawa Yanci. Ya kara da cewa hatta kudaden kasashen a Faransa ake buga su, sannan kuma a dora musu bashi sai sun biya.

Batum bikin shekaru 63 da Najeriya zata cika da samun Yancin Kai, Hon. Tukura ya ce an samu nasarori da yawa na cigaba da habakar tattalin arzikin kasa. In da ya bada misali da Birnin Taraiya Abuja inda ya ce kafin Yancin kasarnan babu shi amma yanzu ya zama birni abun alfahari ga dukkan Yan Najeriya.

Bayan haka. ya ce an samu gine gine na tituna da makarantu da masana’antu da sauran abubuwa na cigaba. Sai dai, ya ce hakan ba yana nufin babu kalu-bale ba na abubuwan more rayuwa.

Hon. Kabir Tukura ya tabbatarwa da Yan Najeriya cewa akwai kyakkyawan fatan cewa Najeriya zata cigaba muddin akwai jajircewa daga dukkan Yan kasa wajen ganin an samar da kyakkyawan shugabanci da zai kai kasar ga inda ake bukatar aje.

Game da aikace-akace da ya gudanar a mazabarsa yace tun lokacin yakin neman zabe ya fahimci irin bukatar mutanen sa kuma haka ya bashi dama ya fito da tsare-tsare na gina al’umarsa ta hanyar samar musu da tallafi da aikace aikace da zasu inganta ruyuwar su.

Yace zai yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin ya kai aiyukan cigaba da za su inganta rayuwar al’umar sa ta fannoni da dama kamar samar da aiyukan yi ga matasa da samar da jari ga mata don bunkasa tattalin arzikinsu wanda hakan zai kawo cigaba da zaman lafiya a Jihar sa.

Har ila yau, ya yi alkawarin cigaba da neman aiyuka da zasu kawo cigaba a mazabar sa kamar tituna da gina makarantu da sauran aiyuka da za su inganta mazabar ta sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here