Home Zirga zirga Jirgin Kamfanin ‘Nigeria Air’ Zai Iso Abuja Yau Juma’a —Hadi Sirika

Jirgin Kamfanin ‘Nigeria Air’ Zai Iso Abuja Yau Juma’a —Hadi Sirika

164
0

Ministan sufuri, Sanata Hadi Sirika ya bayyana cewa jirgin saman kamfanin ‘Nigeria Air’ zai iso Abuja ranar Juma’a wani lamari da zai zama babban ci gaba ga shirye-shiryen soma tafiyar da harkokin kamfanin.

A hirar da ya yi da gidan Talabijin na Channels, ministan ya ce jirgin zai iso ne cikin kwana biyu.

Ya yi alkawarin cewa za a kaddamar da jirgin mai kalolin tutar Nijeriya domin cika duka alkawuran da gwamnatin Buhari ta yi a bangaren sufuri.

Sai dai ya ce abin da ya rage kadai shi ne samar unguwanni kusa da filin jirgin sama wanda zuwa yanzu an kai kashi 60 cikin 100 na aikin.

A cewarsa, an kammala gina tubalin ginin kuma suna neman gwamnati mai zuwa ta karasa aikin samar da unguwannin ta yadda zai saukaka wa mutane hawa jirgin.

Sirika a cikin watan Maris, yayin wani taron masu ruwa da tsaki a bangaren sufuri, ya ce kamfanin ‘Nigeria Air’ zai soma aiki gadan-gadan kafin karshen gwamnatin Muhammadu Buhari.

Da yake amsa tambaya kan takamaimen lokacin da ‘Nigeria Air’ zai soma aiki, ministan ya ce “kafin karshen wannan gwamnati, kafin 29 ga watan Mayu.”

Ya kara da cewa gwamnatin tarayya za ta bar bangaren sufuri cikin yanayi mai kyau fiye da yadda ta tarar da shi kasancewar an cimma fiye da kashi 90 cikin 100 na taswirar da aka tsara cimma a bangaren. (Leadership Hausa).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here