Home Diplomasiyya Jam’iyyatu Ansariddeen Ta Bukaci Kungiyar ECOWAS Da Ta Rungumi Sasanci A...

Jam’iyyatu Ansariddeen Ta Bukaci Kungiyar ECOWAS Da Ta Rungumi Sasanci A Maimakon ‘Yaki

228
0
NIASS G

Kungiyar addinin Musulunci ta Jam’iyyatu Ansariddeen (Attijaniyya), ta yi kira ga Kungiyar Tattalin Arziki ta Kasashen Africa ta Yamma wato ECOWAS da ta rungumi sasantawa a matsayin hanya daya tilo da zai dawo da mulkin Demokradiyya a kasar Nijar a maimakon yin amfani da karfin soji.

Kungiyar ta yi wannan kira ne ta bakin Sakataren ta na Kasa, Muhammad AlQasim Yahaya a wani taro na Yan Jaridu da suka gudanar a hedikwatar Kungiyar da ke Gwarinpa a Birinin Taraiya Abuja.

AlQasim ya ja hankalin Shugabannin Kungiyar Kasashen ECOWAS akan halin da za a shiga idan aka tsunduma yaki; wanda ya ce         tuni ma mutane suna cikin kuncin rayuwa da matsi na tattalin arziki sakamakon takunkumin da aka kakaba musa na daukewar wutar Lantarki a kasar.

Ya ce ‘Yaki zai haifar da mummunar illa ta rayuka da dukiya masu wanda hakan bai dace ba tunda za’a a iya warware kowacce irin matsala ta hanyar zaunaya a tebur domin tattaunawa a samo mafita.

Sakataren Kungiyar ta Attijaniyya ya kara jan hankalin  Kungiyar ECOWAS cewa Demokradiyya ta bawa kowa yanci na fadin albarkacin baki, sabo da haka idan aka zauna kowa zai fadi bukatun sa wandanda za’a iya cimma mafita ba tare da an shiga ‘Yaki ba.

AlQasim ya kara da cewa a maimakon ‘Yaki, gwara a kara kakabawa Sojojin takunkumin Tattalin arziki wanda ya ce watakila zaifi yin tasiri a maimakon a shiga ‘Yaki wanda zan wargaza kasar harma da kasashe makwabta irin su Najeriya.

Kungiyar ta yi kira ga Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu a matsayinsa na Shugaban Kungiyar ECOWAS da ya cigaba da lalubo hanyoyi na sulhu wajen ganin an dawo da mulkin Demokradiyya a Kasar Nijar a maimakon a shiga ‘Yaki.

Attijaniyya ta yaba da kokarin da ya ke yi na tura tawaga da amfani da Karin wasu hanyoyi na ganin an kare martabar Demokradiyya a Kasar ta Nijar.

AlQasim ya ja hankalin Shugabannin juyin Mulkin Nijar da su sani cewa suna mayar da hannun agogo ne bawa; ta hanyar Juyin Mulki wanda Duniya baki daya ta Kaurace masa. Sabo da haka, ‘Juyin Mulki cibaya ne ga kasashen Africa” inji shi.

Ya ce, a matsayin su na Musulmi su sani cewa Musulunci ya haramta Mulki na Danniya da fin karfi; sa bo da haka su yi koyi da koyarwar Addinin Musulunci ta hanyar bayar da kofa wajen Sasantawa wajen ganin an warware dukkan matsalolin da suke addabar Kasar bawai Juyin Mulki ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here