Home Siyasa Jam’iyyar LP Ta Kori Dan Takarar Gwamnanta Na Kano, Bashir I. Bashir...

Jam’iyyar LP Ta Kori Dan Takarar Gwamnanta Na Kano, Bashir I. Bashir Daga Jam’iyyar

193
0

Jam’iyyar LP a Jihar Kano, ta yi watsi da ikirarin cewa Bashir Ishak Bashir, wanda ya koma jam’iyyar APC ne dan takararta na gwamna a Jihar.

A ranar Litinin din da ta gabata ne Ishak-Bashir ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) cewa ya fara tattaunawa da jam’iyyar APC domin mara mata baya a zabe mai zuwa.

“Ina tattaunawa da shugabannin jam’iyyar APC a matakin kasa kan yadda za mu mara wa jam’iyyar baya ta lashe zabe mai zuwa.

Ishak-Bashir ya shaida wa NAN cewa: “Ba da jimawa ba zan tuntube ku kan matsayarmu ta karshe kan lamarin. Shugaban jam’iyyar LP a jihar, Alhaji Mohammed Raji, ya yi watsi da ikirarin Ishak-Bashir, inda ya bayyana cewa ba shi ne dan takarar gwamnan LP a jihar ba.

Raji ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai a ranar Litinin a Kano cewa, sunan Ishak-Bashir bai taba shiga jadawalin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ba a matsayin dan takarar gwamna na LP a Jihar Kano.

 “Ya zo jam’iyyar shi kadai ya bar jam’iyyar ba tare da kowa ba,” in ji Raji.

Ya kara da cewa tsarin jam’iyyar ya ci gaba da kasancewa tare da dukkan ‘yan takararta na Sanata, Wakilai da na Majalisar Jiha da ke takara a babban zabe mai zuwa.

Sai dai ya ce akwai batutuwa a cikin jam’iyyar da suka haifar da rashin hadin kai a cikin manyan mukamai da mambobin jam’iyyar.

Raji ya kara da cewa “Wasu abubuwan da ba daidai ba” sun yi kokarin karkatar da hankalin jam’iyyar tare da yin barazanar sauya sheka.

“Muna ba da shawara sosai ga irin wadannan nau’ikan mutane da su sani cewa mu ‘Masu biyayya’ muna goyon bayan takarar Obi da Dati dari bisa dari a Jihar Kano,” in ji shi.

A halin da ake ciki, wata majiya a jam’iyyar ta ce an mika sunan Raji ga INEC a matsayin dan takarar gwamna na LP a Jihar Kano. (Leadership Hausa).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here