Home Kotu da 'Yan sanda Jajiberen Zabe: Yadda Aka Kama Dan Majalisar Taraiya Da Tsabar Dalar Amurka...

Jajiberen Zabe: Yadda Aka Kama Dan Majalisar Taraiya Da Tsabar Dalar Amurka Kusan 500,000

330
0

Hukumar ’Yan sanda a Jihar Ribas sun cafke dan Majalisa Wakilai mai wakilatar mazabar Fatakwal II, Chinyere Igwe, da tsabar kudi har Dalar Amurka 498,100, ana jajiberin zabe.

A cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Grace Iringe Koko ta fitar, ta tabbatar da kama dan majalisar, wanda dan jam’iyyar PDP ne da yake neman a sake zabensa.

Kazalika, ’yan sandan sun kuma ce sun kama shi da jerin sunayen mutanen da yake shirin raba wa kudin, da nufin sayen kuri’a.

Ta ce tuni Mataimakin Sufeto-Janar (AIG) mai kula da harkokin zabe a Jihar, Abutu Yaro, ya bayar da umarnin zurfafa bincike domin gurfanar da wanda ake zargin a gaban kuliya.

“A yau 24 ga watan Fabarairu da misalin karfe uku na dare, ƴan sandan da ke aiki a jihar Ribas a kan hanyarsu ta zuwa shalkwatar hukumar zaɓe – INEC suka tsayar da motar wani kuma suka gano dalar Amurka dubu 498 da ɗari ɗaya a cikin wata jaka a bayan motarsa,” in ji sanarwar.

A zaɓukan baya, ana zargin ‘yan siyasa da amfani da kuɗi wajen sayen kuri’un jama’a.

A halin yanzu dai ana ƙarancin takardun kuɗi na naira a Najeriya abin da ya jefa ‘yan siyasa cikin zullumi game da yadda za su samu kuɗin sayen ƙuri’a.

Ya kuma bukaci dukkan ’yan takara da jam’iyyun siyasa da su bi dokokin zabe sau da kafa, tare da neman jama’a da su ci gaba da ba jami’an tsaro bayanan sirrin da za su kai ga kama bata-gari.

Hakan na zuwa ne ƙasa da kwana guda kafin babban zaɓen Najeriya, inda al’umma za su zaɓi sabon shugaban ƙasa da kuma ƴan majalisar dokokin tarayya.

Kamun dan majalisar dai na zuwa ne kwana biyu bayan wata kotun majistare da ke zamanta a Fatakwal ta aike da dan majalisa mai wakiltar mazabar Etche/Omuma a Majalisar Wakilai, Ephraim Nwuzi, gidan yari.

An dai yanke Ephraim, wanda dan jam’iyyar APC ne hukuncin bayan ’yan sanda sun zarge shi da tayar da rikicin kabilanci a tsakanin jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here