Home Uncategorized Isra’la ta umarci Falasdinawa su fice daga Arewacin zirin Gaza cikin kwana...

Isra’la ta umarci Falasdinawa su fice daga Arewacin zirin Gaza cikin kwana ɗaya

189
0
Palastinians moved out

Isra’ila ta shaida wa Majalisar Dinkin Duniya cewa dole duk Falaɗinawan da ke Arewacin zirin Gaza su tsallaka zuwa Kudanci cikin sa’oi 24.

Tankokin yaƙin Isra’ila sun ƙara kusantar iyakar Gaza, gabanin afkawa birnin don kawar da mayakan Hamas.

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Gaza ya ce dakarun Isra’ila ne suka gabatar da wannan gargaɗi a cikin daren Alhamis.

Dakarun Isra’ila sun ci gaba da ludugen wuta a Gaza, yayin da aka shiga rana ta biyu da katse wutar lantarki a yankin da Palasɗinawa suke.

Haka nan kuma Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta damu matuƙa da yadda mata masu juna biyu da yawan su ya kai dubu goma sha biyar a Gaza basu samun zuwa asibiti don kula da lafiyarsu, ga kuma rashin ruwa mai tsafta.

Ma’aikatan lafiya sun ce mutane aƙalla 45 aka kashe, yayin da ɗaya daga cikin hare-haren ya rusa rukunin gidaje a Jabaliya.

Wasu daga cikin mutanen da lamarin ya ritsa da su sun shiga gidajen ne don neman mafaka daga luguden bama-baman.

Mutane fiye da dubu daya da dari biyar hare-haren sama na Isra’ila suka kashe tun daga ranar Asabar da ta ƙaddamar da su.

Isra’ila ta ce ba za ta yi sassauci ba kan rufe duk wata hanyar shigar da kayan agaji zuwa Gaza har sai mayaƙan Hamas sun saki waɗanda suka yi garkuwa da su, duk da cewa shirin samar da abinci na majalisar dinkin duniya ya yi gargaɗin samun ƙaracin abinci da ruwa a Gazar.

Dr Mohamad Matar likita ne da ke aiki a asibitin Al-Shifa, babban asibitin Gaza. Ya shaidawa BBC cewa ana cikin mawuyacin hali.

“Mafi yawan mutanen da suka mutu, da waɗanda suka jikka, duk sun sakamakon tashin bama-bamai ne. Mafi yawa sun samu rauni mai hatsarin garke, wasu a kai, wasu a ciki ko ƙirji. Shekara tara kenan ina aiki a Gaza kuma cikin shekarun nan na ga munanan yanayi, amma wannan karon ba a cewa komai. A halin yanzu magani da sauran kayan aikin mu basu da yawa. Idan har aka ci gaba da tafiya a haka to bana zaton za mu iya shawo kan lamarin.” inji Dr Mohammad

Yanzu haka dai Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta damu matuƙa da yadda mata masu juna biyu da yawan su ya kai dubu 50 a Gaza basu samun zuwa asibiti don kula da lafiyar su, ga kuma rashin ruwa mai tsafta.

Ana sa ran fiye da ranbbin su za su haihu a cikin watanni masu zuwa.

Jami’an Majalisar Dinkin Duniyar sun kuma bayyana damuwa da halin da matan za su shiga saboda tsananin fargaba da damuwa. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here