Home Uncategorized Isra’ila ta karɓe iko ta mashigar Rafah a Gaza

Isra’ila ta karɓe iko ta mashigar Rafah a Gaza

104
0
Jirgi ruwan wuta

Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta ƙwace iko da mashigar Rafah ta ɓangaren Gaza – wadda ke iyaka da ƙasar Masar ta ɓangaren kudu.

Haka nan jami’an Masar sun bayyana cewa sun ga sojojin Isra’ila waɗanda tankokin yaƙi ke yi wa rakiya – na sintiri a bakin iyakar ta ɓangaren Gaza, .

Sun kuma bayyana cewa sun ji rugugin bindigogi da ruwan bama-bamai, sai dai lamarin bai yi ƙamari ba.

An kwashe tsawon dare Isra’ila na ruwan wuta a yankin, sa’o’i kaɗan bayan Isra’ila ta yi watsi da yarjejeniyar da Hamas ta amince da ita.

Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta kai hari a birnin Rafah bayan ta ƙi amincewa da buƙatun da Hamas, a tattaunawar neman tsagaita wuta da aka yi.

Isra’il ta ce ba a cika ƙa’iddojin da ta gindiaya ba game da shirin tsagaita wuta, amma ta ce zata tura tawaga birnin Alkhahira domin kara tattaunawa.

Wani ma’aikacin asibitin faladinawa ya ce harin wanda aka shafe dare ana yin, a Gabashin Rafah ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyar.

Tun a ranar Litinin Isra’ila ta rarraba takardun neman Faladinawa su fice daga daga garin Rafah, su kuma koma Arewacin Gaza.

To sai dai a nasa bangare, sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya yi kira ga duk ɓangarorin biyu su mayar da hankali da wanzar da zaman lafiya da kuma kawo ƙarshen yaƙin Gaza.

Ya ce: “A yau ina kira da babbar murya ga Amurka Isra;ila da kuma Hamas, ku ƙara dagewa wajen ƙulla yarjejeniya da kuma wanzar da zaman lagiya. Ina ganin wannan dama ce ta kawo ƙarshen yaƙin Gaza ba tare da wani yunkurin turjiya ba. Ba zamu taba lamuntar kai hari ta ƙasa a birnin Rafah ba.”

Babu dai wani tabbaci a game da makomar dubban Falaɗinawa, musamman, bayan Isra’ila ta basu wa’adin ficewa daga Rafah,

Kasashen duniya dai na ci gaba da kira ga Isra’ila domin ganin ta dakatar da shirin ta na afkawa Rafah ta ƙasa.(BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here