Home Uncategorized Isra’ila da Falasɗinu na zargin juna da kai hari kan asibitin Gaza

Isra’ila da Falasɗinu na zargin juna da kai hari kan asibitin Gaza

147
0
Gaza Hospital Bombing

Fashewar da bam ya yi a asibitin Gaza ya janyo martani daga sassan duniya, inda ƙasashen larabawa da dama ke zargin Isra’ila da aikata laifin yaƙi.

Shugababi da dama sun bayyana lamarin a matsayin kisan-gilla, kuma sun ce Isra’ila ta aikata babban lafin yaƙi.

Hukumomin kinwon lafiya a Gazar sun ce Isra’ila ce ta kai harin bam a asibitin na Al Ahli da ke a birnin Gaza.

Dakarun Isra’ila dai sun musanta cewa su suka kai harin, kuma sun zargi ƙungiyar Palasɗinawa mai iƙirarin jihadi da kai harin.

A na ta ɓangaren ƙungiyar ta bayyana zargin na Isra’ila a matsayin tsabar ƙarya.

Da yake zantawa da BBC kakakin rundunar Isra’ila, Jonathan Conricus, ya musamta hannun ƙasarsa a ciki, yana mai cewa Falasdinawa masu ikirarin jihardi ne suka aikata wannan ɓarna.

Ya ce “Makamin roka da ƙungiyar masu iƙirarin jihadi suka harba ne ya faɗa kan asibitin a bisa kuskure. Muna nazari kan bidiyon wani jirgi marar matuki kuma muna nazari kan sauran abubuwa, nan gaba kaɗan za mu fitar da sautin wayar da aka naɗa ta jagororin Hamas wanda ke nuna cewa suna sane da abin da ya faru.’’

Sai dai a lokacin wani jawabi ga manema labarai, jakadan Falasɗinawa a Majaisar Dinkin Duniya, Riyad Mansour ya ce sojojin Isra’ila ne suka kai harin.

Ya ce “Kamar yadda kuke gani, mu gamayya ce ta ƙasashen Larabawa waɗanda suka damu sosai kan kisan gillar da Isra’ila ta aikata a Zirin Gaza. Mun yi Allah-wadai da wannan ɓarna, kuma dole ne a hukunta duk wanda ke da hannu a wannan aika-aika.

Shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas dai ya sanar da ficewa daga taron da a baya aka tsara yi tsakanin su da shugaba Biden na Amurka.

Da yake zantawa da BBC kakakin rundunar Isra’ila, Jonathan Conricus, ya musamta hannun ƙasarsaa ciki, yana mai cewa Falasdinawa masu ikirarin jihardi ne suka aikata wannan ɓarna.

Ya ce “Makamin roka da ƙungiyar masu iƙirarin jihadi suka harba ne ya faɗa kan asibitin a bisa kuskure. Muna nazari kan bidiyon wani jirgi marar matuki kuma muna nazari kan sauran abubuwa, nan gaba kaɗan za mu fitar da sautin wayar da aka naɗa ta jagororin Hamas wanda ke nuna cewa suna sane da abin da ya faru.’’

Sai dai a lokacin wani jwabi ga manema labarai, jakadan Falasɗinawa a Majaisar Dinkin Duniya, Riyad Mansour ya ce sojojin Isra’ila ne suka kai harin.

Ya ce “Kamar yadda kuke gani, mu ƙungiya ce ta ƙasashen Larabawa waɗanda suka damu sosai kan kisan gillar da Isra’ila ta aikata a Zirin Gaza. Mun yi Allah-wadai da wannan ɓarna, kuma dole ne a hukunta duk wanda ke da hannu a wannan aika-aika.’’

Shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas dai ya sanar da ficewa daga taron da a baya aka tsara yi tsakanin su da shugaba Biden na Amurka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here