Home Ilimi Ilimi shi ne zamu bawa fifiko – inji Hon. Isma’il.

Ilimi shi ne zamu bawa fifiko – inji Hon. Isma’il.

214
0
Zaria a

Daga Hassan Ibrahim

Shugaban kwamitin ilimi na majalisar dokoki na jihar Kaduna ɗan majalisa mai wakiltar cikin birnin Zariya,Hon. Mahmud Lawal Ismail, ya jaddada ƙudirin sa na cigaba da  taimaka wa al’umma musamman kan abinda ya shafi ilimi.

Ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan ganawa da ɗaliban da  ya tallafa musu  na ɗaukan nauyin karatunsu,wanda ya gudana a garin Zariya.

Hon. Mahmud Lawal Isma’il ya bayyana cewa, akwai tsare tsare da mu kayi akan ɓangaren ilimi, da kuma ɓangaren ziyartar makarantu da mu keyi, kasancewar duka muna yi ne ta yanda zamu bada gudummuwar mu ta fannin ilimi.

“Jama’a  sun mana abinda ba za mu saka musu ba sai ta wannan hanyar wannan shine babban manufar mu.Ya ce”

Ya kuma ƙara da cewa, a  lokacin yaƙin neman zabe, munyi alkawura daban daban kuma da yardan Allah zamu cika.

A cewarsa, abu na farko da muka ga ya dace   mu yi haɗin guiwa da malaman wannan cibiya wato (Institute of Education and Information Technology Zaria) domin kawo mutane talatin (80) wanda zamu basu tallafin karatu na shaidar malanta wato (NCE).

Ya bayyana cewa, mun biya wa ɗaliban sakandare masu rubuta jarrabawar  fita na (NBAIS) mutane (70) da masu karatun fannin lafiya su (150).

“Wannan karatun shine mafitar ku,kuma shine alkhairi a gare ku,karatun ne ya kaimu wannan matsayi da muke a yau.ba yanda za’a baka shugaban kwamitin ilimi  in an san ba zaka iya rikewa ba,to  in da gaske muna ƙaunar ku sai mun taimake mu dan kuma ku kai matsayin da ya kai namu.Acewar sa”

Ya kuma shawarce su da cewa dan Allah suyi abinda ya dace, kuma  duk damar da muka samu zamu taimaka muku.

Ya kuma  yi musu fatan alkhairi da kuma roƙon Allah  ya basu  ikon yin karatun.kuma ku kiyaye dokokin makarantar, kuyi abinda ya dace domin cigaban ku da cigaban al’umma baki ɗaya.

Ya na mai cewa, ku sa rai za kuyi dan Allah ne zaku taimakawa kanku,ku taimaka wa addinin ku, sai Allah ya baku lada biyu,ga ladan niyyar abun kirki,ga kuma amfanin karatun da za kuyi.

Inda ya buƙaci al’umma su taya shi  da addu’a domin ƙoƙarin sauke alƙawuran da ya ɗauka.

domin acewarsa duk abinda muke yi ba iya wanmu bane addu’ar jama’a ne.

Kazalika,Mansur Lawal daga gundumar Ƙaura da Zainab  Aliyu daga gundumar Kwarbai A na daga cikin  ɗaliban da suka amfana da wannan tallafi,sun nuna jin daɗin su  da godiya da ɗan majalisar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here