Home Kotu da 'Yan sanda Hukumar Kwastam ta Najeriya ta kama tufafin sojoji da ƙwayoyi masu yawa

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta kama tufafin sojoji da ƙwayoyi masu yawa

164
0

Hukumar kostom mai yaƙi da fasa ƙwauri da ke a filin jirgin sama na Murtala Muhammad a birnin Legas, ta kama tufafi da sauran kayayyakin sojoji da na ‘yan sanda waɗanda take zargin an shigo da su daga Afirka ta kudu, ba bisa ka’ida ba.

Babban jami’in hukumar mai lura da tashar jirgin saman na Legas Bello Kaniyal Dangaladima, ya shaida wa BBC cewa daga cikin kayyakin da aka kama har da Riguna da hulunan kwano na sojoji, da kayayakin ‘yan sanda

Ya kuma ce akwai kuma nau’in ƙwayoyin Tramadol da ake kira (aji garau)da kuɗinsu ya haura naira biliyan talatin da bakwai da aka shigo da su daga ƙasashen Indiya da kuma Pakistan.

Wannan kame dai na zuwa a daidai lokacin da Naijeriya take shirin gudanar da babban zabe na shugaban kasa a watan Gobe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here