Home Labaru masu ratsa Zuciya Hatsarin Taraba: Har Yanzu Ana Neman Mutum Sama Da 70 – NEMA

Hatsarin Taraba: Har Yanzu Ana Neman Mutum Sama Da 70 – NEMA

162
0
NEMA RESCUE

Ya zuwa yanzu hukumomin yankin sun tabbatar da mutuwar mutum 17 yayin da aka ceto mutum 14.

Kwale-kwalen na dauke da ‘yan kasuwa da ke dawowa daga kasuwar kifi da ke gundumar Ardo-Kola ta jihar Taraba da yammacin ranar Asabar lokacin da ya kife a Kogin Benue, wanda shi ne daya daga cikin ruwa mafi girma a Najeriya, in ji hukumar agajin gaggawa ta kasa.

Fiye da fasinjoji 100 ne ke cikin jirgin, sannan an samu ceto 14, yayin da aka gano gawarwaki 17, amma kuma mutane 73 suka bace, kamar yadda shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya, Ladan Ayuba, ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press.

Gwamnan jihar Taraba Agbu Kefas ya kwatanta hatsarin a matsayin babban abin takaici kuma ya ba da umarnin amfani da rigunan ceto ga fasinjojin kwale-kwale.

“Ruwan kasarmu, wanda shi ne daya daga cikin mafi dadewa a yankin, ya kamata ya zama tushen arziki ne ba na mutuwa ba,” in ji gwamnan, a cewar wata sanarwa da gwamnan ya fitar ranar Litinin.

Ibtila’in kifewar kwale-kwale na kara zama ruwan dare a cikin a tsakanin al’ummomi da ke yankunan karkara a duk faɗin kasar wacce ke Afirka ta Yamma.

Wannan shi ne hatsari na uku da ya shafi fasinjoji sama da 100 cikin watanni hudu kacal. Yawanci ana danganta hadurran da daukar nauyi da ya wuce kima. Babu hanyoyin mota masu inganci a ire-iren wadannan yankuna.

Jami’an tsaro na gudanar da bincike don gano musabbabin faruwar wannan hatsarin, in ji kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba Usman Abdullahi. Mazauna yankin da masunta suna taimakawa hukumomin ceto.

Abdullahi ya ce yana fargabar cewa aikin binciken na iya daukar kwanaki kafin a kammala saboda kogin yana ganiyar tumbatsa.

“Ba ma tsammanin za mu samu gawarwakin a kusa da nan,” in ji shi. (Muryar Amurka).

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here