Home Tsaro Harin Bomb A Gwoza: Kun Hana Ni Tafiya Aljanna – In ji...

Harin Bomb A Gwoza: Kun Hana Ni Tafiya Aljanna – In ji Daya Daga Cikin Wadanda Su Ka Kai Harin

78
0
20231102 145959

Daya da ga cikin wadanda su ka kai harin bomb a Gwoza da ke Jihar Borno ta baiyana takaicinta na hanata yunkurin kashe Kanta da Sojoji su ka yi na hanata tafiya Aljanna ta hanyar tayar kunan Bakin Wake a ranar Asabar da ta gabata.

Dan Majalisar Taraiya mai Wakiltar Borno ta Kudu, Sanata Ali Ndume ya sanar da cewa daya da ga cikin wadanda a ka hana tayar da bomb din wata yarinya yar shekara kimanin 20 ta nuna takaicin ta na hanata yin taraiya da yan uwanta na zuwa Aljanna.

Sanata Ndume wanda ya ke karawa Yan Jaridu haske a kan yadda harin kunan Bakin waken ya kasance ya ce yadda a ka yi a ka gano yarinyar kafin ta tayar da bomb din shi ne an umarci duk mutaten da su ke yankin da su shige gidajen su amma ita yarinyar tun da ba yar yankin ba ce sai ta rasa gidan da za ta shiga wanda hakan ya bawa jami’an Soji dama su ka kamata kafin ta tashi bomb din.

Ya kara da cewa yaran da su ka kai harin dukkanin su mata ne yan kimanin shekaru 20 wadanda an yi musu huduba da cewa idan sun mutu aljanna za su tafi kuma an sa su sun yi aski da kwalliya ta tafiya Barzahu.

Sanata Ali Ndume ya yabawa Sojojin da su ke yankin na kokarin da suka yi na ganin sun yi aikin su cikin kwarewa da kamala duk da irin kalubale da su ke fuskanta na rashin kayan aiki na zamani da kyakkyawan yanayi na gudanar da aikin na su.

Suma mutanen yankin, ya yaba mu su na jajircewa da su ka nu na da rashin dimaucewa duk da cewa sun rasa rayukan yan uwansu da jikkata na mutane da dama.

Tunda fari, Sanata Ali Ndume ya gabatar da Kuduri na gaggawa a gaban Majalisar Dattawa akan harin da aka kai a Gwoza wanda ya yi sanadiyyar rasuwar sama da mutum 30 da jikkata sama da mutum 40.

Wanda Majalisar ta Dattawa ta yi kira ga Gwamnatin Taraiya da ta samar da kayan yaki na zamani wajen yakar ta’addanci a Yankin  Arewa maso Gabas da ma Najeriya baki daya a wani mataki na kawo karshen batum.

Sannan kuma, Majalisar ta umarci Hukumar agajin gaggawa ta NEMA da ta samar da tallafi ga mutanen da suka rasa yan uwansu da wadanda su ka jikkata a wani mataki na saukaka mu su rashin da su ka yi. Sannan kumu, Majalisar ta yi shiru na minti daya domin nuna alhininta a kan rashin da a ka yi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here