Home Tsaro Hare-haren masu iƙirarin jihadi sun ƙaru a Nijar – Rahoto

Hare-haren masu iƙirarin jihadi sun ƙaru a Nijar – Rahoto

197
0
Nijar Yan ta'adda

Rahotanni na nuna cewa harkokin tsaro sun ƙara taɓarɓarewa a Nijar, musamman a yankunan da ake fama da hare-haren ‘yan bindiga masu iƙirarin jihadi, mako uku bayan da sojoji suka hamɓarar da gwamnatin Mohamed Bazoum.

Shafin LSI-Africa, da ke birnin Paris na Faransa ya ruwaito cewa tun bayan da sojojin suka yi juyin mulki alamu sun nuna cewa an janye dakarun ƙasar da ke fagen daga a yankuna daban-daban, wanda hakan kila ba ya rasa nasaba da ƙoƙarin da sojojin ke yi na tattara ƙarfinsu wajen kare babban birnin ƙasar Yamai, domin kawar da duk wata barazana ta ƙin amincewa da sauyin gwamnatin.

Ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka ECOWAS ko CEDEAO ta yi barazanar ɗaukar matakin soji domin mayar da hamɓararren shugaban ƙasar, idan har sojojin ba su mayar da shi cikin lumana ba.

Ana ganin wannan mataki na ƙungiyar ƙasashen maƙwabta, wanda ya haifar da zaman ɗar-ɗar, da kallon hadarin-kaji tsakanin sojin da suka karɓe mulki da ƙungiyar, ya sa sojojin janye dakarun daga fagen daga domin haɗa ƙarfinsu a babban birnin don kare mulkinsu.

Bayanai sun nuna cewa a dalilin rashin dakarun su kuma mayaƙa masu tayar da ƙayar baya suka samu damar kai ƙarin hare-hare a yankunan.

Tsawon shekara da shekaru dakarun Nijar na fama da mayaƙa masu tayar da ƙayar baya da ke iƙirarin jihadi a yankin Tafkin Chadi na kudu maso gabashin ƙasar da kuma yankin da ya ƙunshi iyakokin ƙasashen Mali da Burkina Faso da ke yamma.

A yankin Tillabery da ke yammacin ƙasar ta Nijar, mayaƙa masu iƙirarin jihadi sun kai hare-hare aƙalla guda shida tun bayan juyin mulkin na ranar 26 ga watan Yuli, inda rahotanni suka ce sun kashe sojoji 28.

podcast promotion

Waɗannan hare-hare sun shafi garuruwn Goulbal da Wabila da Hondobon da Katanga da Samira, da kuma Sanam.

Sai dai rahoton ya ce babu cikakken bayani a kan harin Sanam, abin da ya sa ake ganin yawan sojin da masu da’awar jihadin suka kashe ka iya ƙaruwa.

Shafin da ya ruwaito labarin ya ce tun bayan zaɓen Mohamed Bazoum, ba a taba kai wa Nijar, hare-haren masu da’awar jihadi da yawa ba cikin ɗan taƙaitaccen lokaci kamar wannan.

Alƙaluma sun nuna cewa hare-haren da aka kai a ƙasar a dan wannan tsakanin sun ninka waɗanda aka kai a lokacin mulkin Bazoum biyu.

Ƙungiyar IS ta lardin Sahel, ita ce ta fi karfi da tasiri a cikin masu tayar da kayar baya da sunan jihadi a yammacin Nijar.

Bayan wannan kungiyar akwai kuma Jamaat Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM), wadda take da alaka da al-Qaeda, wadda ita ma ana ganin tana kai hare-hare a wannan yanki

Haka can ma a gabashin ƙasar ƙungiyar Jama’atu Ahlis Sunna Lidda’awati wal-Jihad, wadda ake wa laƙabi da Boko Haram, bayanai sun ce ta ƙara ƙarfi tun bayan juyin mulkin.

A sanadiyyar janye sojojin daga fagen daga domin su je su kare masu juyin mulkin, ‘yan ƙungiyar sun samu damar karƙar maƙudan kuɗae daga mazauna garuruwan da suke, in ji kafar yada labaran.

Shafin ya ruwaito cewa, bayanin da ya samu ya nuna cewa mayaƙan masu iƙirarin jihadi sun karɓi kuɗin da ya kai dalar Amurka 13,320 a Turban, yayin da a ƙauyen Morey suka kari abin da ya kai dala 6,700, sai dala 10,000 a Madouri da kuma dala 8,300 a Kargamdi.

Can a garin Gagamari, mayaƙan na Boko Haram sun nemi a ba su kuɗin da ya kai dalar Amurka 83,000, yayin da hukumar wajen ta ce dala 10000 za ta bayar.

Mayaƙan sun ƙi amincewa da wannan ragi, kamar yadda suka ƙi yarda da dala 8300 da al’ummar garin Chetimari suka ce za su biya.”

Shafin labaran ya ce, masu tayar da ƙayar bayan sun yi amfani da wannan dama inda ko dai suka sace ko kwashe ko kuma lalata motoci da makamai da harsasai da yawa a waɗannan yankuna.

Shugaban gwamnatin mulkin sojin Birgediya Janar Abdourahmane Tchiani, ya ce sun hamɓarar da gwamnatin Bazoum ne saboda abin da ya kira taɓarɓarewar tsaro.

Sai dai shafin labaran na intanet na LSI-Africa, ya nuna wasu alƙaluma na hukumomin Nijar din game da hare-hare, waɗanda ke nuna cewa an samu raguwar yawan farar hula da hare-haren ke rutsawa da su da kashi 60 cikin ɗari a 2022 sannan an samu raguwar da kashi 69 cikin ɗari a 2023, idan aka kwatanta da shekarar 2021

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here