Home Sadarwar Zamani Harajin Tsaron Yanar Gizo-gizo: Yan Najeriya Ku Sha Kurumin Ku, Ba Mai...

Harajin Tsaron Yanar Gizo-gizo: Yan Najeriya Ku Sha Kurumin Ku, Ba Mai Cire Mu Ku Ko Sisi – Inji Majalisar Wakilai

128
0
Reps Renoveted Chamber

Majlisar Wakilai ta  yiwa Yan Najeriya albishir cewa ba za a cirewa kowa ko kobo ba da ga cikin asusun bankin sa sakamakon Dokar nan ta Tsaron Yanar Gizo-gizo da Majalisar ta amince da ita.

 

Shugaban Kwamitin Tsaro da Bayanan Sirri na Majalisar Wakilai Hon. Satomi Alhaji Ahmed ne ya bayar da wannan tabbacin a yayin da ya ke yiwa Yan jaridu karin haske akan Dokar.

 

Ya ce wadanda za a cirewa harajin rabin  kaso wato (0.5%) sun hada kamfanonin Sadarwa (MTN, GLO, AIRTEL etc) da kamfanonin Sayar da “Data” da na Inshora da masu POS da  Hukumar hada-hadar kudade wato SEC da bankuna na kasuwanci.

Hon. Satomi

Sabo da haka ya ce “Yan Najeriya ku sha kurumin su ba za a cirewa kowa ko sisi ba daga cikin asusun bankunan ku sakamakon wannan Doka.

 

Satomi ya ce wadannan kudade da za a cira za’a yi amfani da su ne wajen inganta batum tsaro baki daya a Najeriya. In da ya ce Dokar an kirkiro ta ne tun shekara ta 2015 amma ba’a saka kason da za a rinka cirewa ba ne shi ya sa Majalisar ta dawo da Dokar don sa ka kason.

 

Ya ce kududen za a rinka tara su ne a babban bankin Najeriya, in da ita kuma Majalisar Taraiya za ta rinka kasafta Kudin duk lokacin da a ka zo kasafin kudi na kowacce shekara domin bawa ofishin Mai bawa Shugaban Kasa Shawara akan harkar Tsaro dama na kashe kudaden a harkar Tsaro Yanar Gizo-gizo dama Tsaro baki daya.

 

Ya bayar da misali da kasashen Belgium da Saudi Arabia wadan da ya ce su na kashe linkin kasafin kudin Najeriya har sau biyu a kan Tsaron Yanar Gizo-gizo. Sabo da haka y ace abun kunya ne a ce Najeriya bata da irin wannan tsari ganin yadda a ke amfani da Yanar Gizo-gizo wajen damfarar mutane kudade masu yawa.

 

A na sa Karin hasken Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Wakilai, Hon. Ali Isa JC cewa ya yi bankin Najeriya ya yi kuskure wajen sanar da cewa za a rinka cirewa Yan Najeriya wadannan kudaden sabo da haka ne su ka ja hankalin sa cewa ba haka Dokar take nufi ba domin su, su kayi Dokar.

Hon. JC

Hon. JC y ace Ministan Shari’a ne kuma Babban Lauyan Gwamnatin Taraiya yak e da alhakin fassara Dokar ba Babban Bankin Najeriya ba. Sabo da haka ne su ka ja hankalin Bankin da ya janye kalaman sa. A koma a yi amfani da Dokar kamar yadda Majalisar ta tsara ta.

 

Ya ce Majalisar Wakilai ba zata saka ido ba ta ga an cutar da Yan Najeriya sabo da haka ne su ka ja hankalin Babban Bankin Najeriya cewa ya mayar da hankalin sa akan kamfanoni da Dokar ta lissafa cewa su ne za su rinka biyan wannan haraji.

 

Hon. JC, ya ce tuni Yan Najeriya su na cikin wani hali na matsin tattalin arzikin sakamakon cire tallafin Man Fetur da Karin kudin wutar Lantarki. Sabo da haka ba za su saka ido ba su ga a na cizgunawa Yan Najeriya da wani Karin haraji.

 

Sai dai Dan Majalisar ya ce wannan haraji da za a rinka cirewa zai taimaka mutuka wajen magance matsalar Tsaro da ta addabi Kasarnan. In da ya ce idan an sami ingantaccen Tsaro zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin Yan Najeriya ta fannoni da dama.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here