Home Zirga zirga Gwamnatin Tarayya Ta Rage Kudin Sufuri Da Kaso 50% Cikin 100 Da...

Gwamnatin Tarayya Ta Rage Kudin Sufuri Da Kaso 50% Cikin 100 Da Na Jiragen Kasa Kyauta

119
0
Lagos Kano train service

Daga yau (Alhamis), ‘’yan Najeriya masu son yin bulaguro za su iya shiga motocin bas na gwamnati a bisa rangwamen kashi 50% na farashin da ake biya a halin yanzu da kuma na jiragen kasa kyauta.” Inji Alake

 

A wani mataki domin saukakawa al’ummar kasar, Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da rangwamen kaso 50 cikin 100 na kudin sufuri da zirga-zirgar ababen hawa a fadin kasar, da kuma sufuri kyauta na illahirin jiragen kasa da ke kasar daga ranar 21 ga Disamba, 2023, zuwa ranar 4 ga Janairu, 2024.

Wannan mataki ya zo ne sakamakon yunkurin gwamnatin tarayya na ganin ta saukaka ma ‘yan kasa musamman a irin wannan lokaci na bukukuwan karshen shekara.

Ministan Ma’adinai na kasa, Dele Alake ne ya sanar da hakan yayin wani taron manema labarai a babban birnin tarayya Abuja.

“A bisa haka ne gwamnatin tarayya ke sanar da cewa tun da ga gobe (Alhamis) za a yi rangwame na musamman a lokacin hutu a kan ababen zirga-zirga da na sufurin jirgin kasa a fadin Najeriya.

Abin da hakan ke nufi shi ne, da ga gobe (Alhamis), ‘’yan Najeriya masu son yin bulaguro za su iya shiga motocin bas na gwamnati a bisa rangwamen kashi 50% na farashin da ake biya a halin yanzu da kuma na jiragen kasa kyauta.” Inji Alake

A lokacin taron na manema labarai, Ministan da ya kasance a matsayin shugaban kwamitin na hadakar ma’aikatun gwamnatin tarayya na tallafin gwamnati mai mambobin da suka hada da Alhaji Mohammed Idris, Bayo Onanuga da Saidu Alkali sun yi karin haske game da shirin inda suka kara jaddada kudurin Shugaban Kasa na ganin ya saukaka rayuwar al’umma musamman irin wannan lokaci na bukukuwa.

Haka zalika, kwamitin ta kara da cewa, wannan matakin ya biyo bayan kyawawan manufofin shugaban kasa na ganin ya taimakawa al’umma masu tafiye-tafiyen hutun karshen shekara domin haduwa da ‘yan uwa da abokan arziki.

Kwamitin ya kara da cewa “wannan tsari zai fara aiki ne a gobe Alhamis 21 ga watan Disamba, kuma zai karkare a ranar 4 ga watan Janairu, 2024.”

Gwamnatin tarayya ta Ma’aikatar Sufuri za ta hada kai da masu sufuri, Kungiyoyin Sufurin Tituna, da kuma Kamfanin Jiragen Kasa na Najeriya domin cimma wannan shiri na musamman na shugaban kasa”

Alake ya bayyana jajircewar Shugaba Tinubu wajen ganin cewa ‘yan Najeriya sun ci moriyar wannan shiri ta wajen taimaka masu na rage kashe kudaden sufuri domin tafiye-tafiye.

“A irin wannan lokaci na bukukuwan Kirsimeti da nuna soyayyarsa ga ‘yan Najeriya, Shugaban Kasa Tinubu ya yi imanin cewa ya kamata gwamnatin tarayya ta fitar da wani shiri domin saukaka tsadar zirga-zirgar jama’a.” inji Alake

Wannan umurni na gwamnati dai ya hada da manyan cibiyoyin zirga-zirga tsakanin jihohin kamar Abuja, Legas, Kano, Kaduna, Enugu, Fatakwal, Owerri, Badan, Akure, Maiduguri, Sakkwato, da sauransu.

Bugu da kari, Shugaba Tinubu ya umurci hukumomin tsaro da suka hada da ‘yan sanda, da DSS, da sojoji su tabbatar da zaman lafiya ba tare da tauye lafiyar ‘yan kasa ba.

A karshe, Minista Alake ya bukaci ‘yan Najeriya da su kasance masu bin doka da oda, da kiyaye tsaro, da tausaya wa juna.

Irin wannan lokaci na bikin Kirsimeti, lokaci ne da al’umma ke amfani dashi wajen nuna kauna, zumunci, hadin kai da taimakekeniya. Babu shakka, wannan mataki na gwamnati zai taimaka matuka musamman wajen baiwa marasa hali damar ziyara da nuna kauna ga ‘yan uwa da abokan arziki tareda da saukaka radadin matsi da ake ciki a kasa musamman a fannin sufuri. (Muryar Amurka).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here