Home Muhalli Gwamnatin Najeriya za ta ginawa wasu ‘yan ƙasar gidaje 5000 kyauta

Gwamnatin Najeriya za ta ginawa wasu ‘yan ƙasar gidaje 5000 kyauta

235
0
ATM Gwarzo

Gwannatin Najeriya ta ce tana shirin gina gidaje dubu biyar-biyar a dukkan shiyyoyi shida na kasar, don bunkasa samar da gidaje.

Ƙaramin ministan gidaje da raya karkara na Najeriya Alhaji Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo ne ya bayyana haka yayin wata tattaunawa da BBC dangane da bikin ranar inganta wuraren zama da gidaje na wannan shekara.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ɓullo da wannan rana ne da manufofi daban-daban ciki har da rage yawan tururuwar al’umma zuwa birane.

Gwamnatin Najeriya ta ce dama akwai wannan tsari na gina gidaje a ƙasar, amma kasancewar wannan ma’aikatar a baya tana ƙarƙashin ma’aikatar ayyuka da makamashi. Amma yanzu an cire ta daga nan kuma za ta fara aiki gadan-gadan.

“Muna da shirin gina gidaje dubu dai-dai a kowacce jiha. Muna jiran Shugaban ƙasa ya sahhale mana ne sannan mu ƙaddamar da aikin.

“Akwai tsarin bai wa waɗanda ba su da gata kyauta, wasu kuma a ba su cikin farashi mai sauki,” in ji T Gwarzo.

Ministan ya ce sun kammala tsare-tsare da zane-zanensu, iyakaci su ƙaddamar da wannan aiki nan ba da jimawa ba.

Ya ƙara da cewa aikin na da fuska biyu, na farko akwai wanda ake kira ‘Mega City’ wato manyan birane, shi ne za a gina gidaje dubu biyar a kowacce shiyya ta Najeriya.

FG Gidaje Kyauta

Amma ya ce faruwar aikin ta ta allaƙa ne da gabatar da kasafin kuɗi wanda za a yi nan ba da jimawa ba.

Ka shi na biyu shi ne, na raya karkara, wanda za a je ƙananan hukumomi a yi hanyoyi a fitar da titi da kasuwanni ta yadda za su zama kai ɗaya da birane, kamar yadda ministan ya bayyana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here