Home Kotu da 'Yan sanda Gwamnatin Najeriya Na Neman Gwamnoni Su Saki Kashi 30 Na Fursunoni A...

Gwamnatin Najeriya Na Neman Gwamnoni Su Saki Kashi 30 Na Fursunoni A Jihohi

209
0

Ministan harkokin cikin gida na Najeriya ya ce yana shirin ganawa da gwamnonin jihohi na ƙasar don cimma matsaya kan sakin aƙalla kashi 30 cikin 100 na fursunoni daga gidajen yarin da ake tsare da su a faɗin ƙasar.

Mista Rauf Aregbesola ya bayyana hakan lokacin da yake magana yayin wani taron ƙara wa juna sani da kamfanin labarai na Najeriya, NAN, ya shirya a Abuja.

Ministan ya ce yunƙurin ya zama dole saboda kashi 90 cikin 100 na mutanen, ana tsare da su ne sakamakon karya dokoki daban-daban na jihohin.

Haka nan, ya ce fiye da kashi 70 cikin 100 na fursunoni 75,635 da ake tsare da su yanzu haka jiran shari’a suke yi.

Ƙasa da kashi 10 cikin 100 ne kawai na fursunonin suka karya dokar gwamnatin tarayya, a cewar ministan.

“Rage cunkoso a gidajen yari 253 a faɗin Najeriya ya zama dole saboda bai kamata wasu daga cikin fursunonin su ci gaba da zama a gidan yari ba,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here