Home Noma da Kiwo Gwamnatin Jigawa ta rage kuɗin takin zamani daga dubu 26 zuwa 16

Gwamnatin Jigawa ta rage kuɗin takin zamani daga dubu 26 zuwa 16

245
0
Gwamnan Jigawa Namadi

Gwamnan Jihar Jigawa da ke a arewacin Najeriya Alhaji Umar Namadi ya ce sun gama tanadin taimakawa monama a jihar domin rage musu raɗaɗin cire tallafin man fetur da aka yi.

Cikin wata tattaunawa ta musamman da ya yi da BBC Gwamna Namadi ya ce matakin farko da suka ɗauka shi ne rage farashin takin zamani daga naira “dubu ashirin da shida zuwa dubu sha shida”.

Gwamnan ya ce suna sane da irin ƙalubalen da cire tallafin mai ya haifar wanda hakan ya jefa mutane cikin matsi, amma suna da fatan hakan zai zamarwa mutanen Najeriya alheri a gaba.

Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da Gwamnatin Tarayyar ƙasar ta sanar da shiri fara raba hatsi a faɗin ƙasar domin ragewar al’umarta zafin halin da cire tallafin ya jefa su.

Har ila yau, suma gwamnatocin jihohi a matsakansu suna da nasu tsare-tsaren da suke shiryawa waɗanda za su yi daidai da buƙatar mutanen da suke wakilta.

“Kowacce jiha ta tsara abubuwa da yawa da za a yi, yanzu misali mu jihar Jigawa, jiha ce ta manoma don haka tanadinmu na taimakawa manoma ne.

“Za mu samar musu da abubuwa cikin sauƙi domin su samu su yi noma cikin sauƙi, abinci ya wadata, domin samun abinci wadatacce shi ne zai rage halin da ake ciki a yanzu.

“Na farko dai mun karya farashin taƙi daga 26,000 zuwa 16,000, kuma mun ɗauki matakai masu tsauri kan cewa sai manomi na ƙasa ne aka amince a sayarwa da takin,” in ji Gwamna Alhaji Umar Namadi.

Gwamnan ya ce sun ɗauki matakin tantance waɗannan manoma na ƙasa sama da yadda ake tsammani, domin dai wannan tsari da aka yi don su ya ishe su.

Ya ce sun samar da kwamiti a duk inda za a sayar da wannan taki, wanda ya haɗa mutane kamar : sarakunan gargajiya da masu anguwanni da bulamai da ‘yan ƙungiyoyin taimakawa al’umma.

Da wuya cikin waɗannan mutane su gaza sanin wanda yazo sayan wannan taki, sai sun bayar da bayanin cewa mutamin gari kaza ne kuma manomi ne, kuma ya kamata a sayar masa takin nan.

“Ko wanene kai ba za a sayar maka da takin nan sama da taki biyar ba, kuma dukka jami’an tsaro a jihar Jigawa mun shaida musu ko wa aka gani da sama da taki biyar a mota a kama shi.

“Ba ma son wannan taki ya fita daga jihar Jigawa, domin an yi tsarin ne ga manoman jihar don kuma su amfana,” in ji Gwamna Namadi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here