Home Labaru masu ratsa Zuciya Girgizar-ƙasa ta kashe sama da mutum 2,300 a Turkiyya da Syria

Girgizar-ƙasa ta kashe sama da mutum 2,300 a Turkiyya da Syria

177
0

Rahotanni na cewa an ƙara samun girgizar ƙasa karo na biyu cikin kwana guda a kudu-maso-gabashin Turkiyya.

Hukumar lura da yanayin ƙasa ta Amurka ta ce ƙarfin girgizar ƙasar ya kai 7.5 a kan ma’auni.

Lamarin ya faru ne a gundumar Elbistan na lardin Kahramanmaras.

Wani jami’in Hukumar Lura da Bala’o’i na Turkiyya ya tabbatar da cewa “wannan wata sabuwar girgizar ƙasa ce ba ragowar wadda ta faru ne a farko ba.”

Ya zuwa yanzu alƙaluma sun nuna cewa sama da mutum 2,000 ne suka mutu sanadiyyar girgizar ƙasar.

Wani faifan bidiyo ya nuna yadda mutane ke gudu cikin ruɗewa a lokacin da girgizar ta biyu ta faru.

An ga mutanen suna ihu, suna gudu a kan tituna a lokacin da ƙura ke lafawa bayan gine-gine sun rufta.

Mutane sama da 1,700 sun mutu a Turkiyya da Syria sakamakon girgizar kasa mai karfi da ta afkawa gidajen jama’a.

Girgizar kasar mai karfin maki 7.8 ta afkawa yankin Gaziantep da ke kudancin Turkiyya a tsakiyar dare.

Kuma an jiyo ruguginta har daga Gaza. An kuma samu rushewar gidaje a Lebanon.

Turkiyya dai ta ayyana dokar ta baci tare da kira ga mutane su dakatar da amfani da wayoyinsu, saboda masu aikin agaji su samu damar kai wa ga wadanda suka makale a cikin baraguzai.

A 1999, irin wannan mummunar girgizar kasar tayi ajalin mutane dubu 17.(BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here