Home Mulki Gina Titunan Kasarnan: Zamu Tabbatar Gwamnatocin Jihohi Da Na Taraiya Sun Yi...

Gina Titunan Kasarnan: Zamu Tabbatar Gwamnatocin Jihohi Da Na Taraiya Sun Yi Aiki Tare – Majalisar Dattawa

148
0
Sen. Hussaini

A yunkurin ta na ganin an samu cigaba cikin sauri wajen gyarawa da gina sababbin tituna da suke Kasarnan; Majalisar Dattawa ta sha alwashin ganin an sami kyakkyawar fahimta da aiki tare tsakanin Jihohi da Gwamnatin  Taraiya.

Shugaban Kwamitin Aiyuka na Tituna  wadanda ake kira FERMA  na Majalisar Dattawa, Sanata Babangida Hussaini Dan Majalisar Taraiya da ya ke Wakiltar Jigawa Arewa maso Yamma ne ya sanar da haka a hirar sa da Yanjaridu a ofishin sa da ke Majalisar Kasa a yau Litinin.

Ya ce akwai tituna kimanin murabba’in Kilomita dubu 38 mallakar Gwamnatin Taraiya a kasarnan; sabo da haka akwai bukatar a samu kyakkyawar fahim ta tsakanin Jihohi da Gwamnatin Taraiya wajen ganin an kula da titunannan tare gina su cikin sauri ba tare da wata matsala ba.

Sanata Hussaini, ya ce tuni an sami wannan fahimta tsakanin Gwamnatin Oyo da Gwamnatin Taraiya in da Jihar ta gina titi ita kuma Gwamnatin Taraiya ta mayar mata da kudin da ta kashe. “Ko da ya ke wannan ba sabon tsari ba ne amma muna so a samu fahimta tsakanin su ta yadda za’a gina tare da gyara wadannan tituna cikin sauri lura da yadda titunan sun lalace da yawa”.

Sanatan ya kara da cewa Kwamitin sa ya na ta ganawa da ma su ruwa da tsaki akan titunan Gwamnatin Taraiya domin a samu fahimtar juna ta yadda za a samu gagaramin cigaba cikin sauri na gyara titunan domin kowa yana amfana da titi kuma idan titi ya na da kyau zai taimaka wajen kawo cigaba ga jama’a.

Ga me da Kasafin Kudi na Shekara ta 2024 da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar ga Majalisar Taraiya; Sanatan ya nu na gamsuwar sa a bangarori guda uku wadanda suka hada da  Samar da Horo ga Matasa da Tallafawa marasa karfi da kuma ware kaso mai tsoka domin gudanar da Manyan Aiyuka.

Ya ce wadannan bangarori su na da muhimmanci so sai wajen kawo cigaba a kasa sannan ganin yadda ake fama da matsi na tattalin arziki in da ya ce tallafawa mabukata da jari tare da koya mu su sana’a zai taimaka ga ya wajen farfado da tattalin arzikin kasarnan.

A bangaren Manyan aiyuka kuwa, Sanata Hussaini ya ce Shugaban Kasar ya yi namijin kokari wajen saka kaso mai tsoka ga manyan aiyuka fiye da yadda aka saba sakawa a baya. Ya ce hakan, zai taimaka kwarai da gaske wajen kawo cigaba ta fannoni da dama.

Da ga kar she, Sanatan ya ce Majalisar Taraiya za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta sa ka ido domin aiywatar da dukkan abubuwan da aka ce za a yi a kasafin kudin. Kuma za su fara ne tun da  ga tattaunawa da Shugabannin Ma’aikatun Gwamnatin Taraiya tun kafin amincewa da Kasafin Kudin domin su tabbatar da cewa an yi abun da ya da ce.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here