Home Tsaro Ganawa da Hafsoshin Tsaro: “Ni Ma Ina Cikin Firgici, Abun Allah Ya...

Ganawa da Hafsoshin Tsaro: “Ni Ma Ina Cikin Firgici, Abun Allah Ya Sawake” In Ji Sanata Wadada

126
0
20240213 213408

Bayan da Majalisar Datttawa ta shafe kimani awoyi goma su na ganawa da Hafsoshin Tsaron, sun gamsu cewa a na kokarin amma akwai bukatar a kara kokari don magance matsalar tsaro da ta addabi kasarnan.

 

Dan Majalisar Datttawa mai Wakiltar Nasarawa ta Yamma , Aliyu Ahmad Wadada ne ya sanar da haka a hirarsa da Yan Jaridu jimkadan da kammala taron ya ce sun gano cewa matsalar tsaro ta na alaka da abubuwa da yawa wandanda sun hada da tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayan masarufi da tashin Dalar Amurka da sauran su.
Sa bo da haka, Majalisar ta amince cewa dole a nemo mafita a cikin gida domin idan aka ce a shigo da abinci da  ga waje dole zai kara haifar da matsalar tashin Dalar Amurka kuma manomam mu na cikin gida za a kashe mu su gwiwa.
Ya ce,  ba abinci ba ne a kasarnan ba bu, akwai abinci sai dai Talakawa ba su da kudin da za su sayi abincin. Sa bo da haka dole gwamnati ta lalubo mafita yadda Talakawa za su sami sauki.
Wadada ya kara da cewa matsalar ta shin Dalar Amurka dole sai masana’antun mu sun koma su na aiki don sarrafa kayayyakin da mu ke samarwa don a fitar da su, su kawo mana kudadenshiga.
Ya ce gwamnati ta ce tana daukar matakai amma ba su san irin matakai da ta ke dauka ba na kawo saukar farashin Dala da sauki na matsin tattalin arziki da  ya addabi Yan Najeriya ba.
Ga me da matsalar tsaro ya ce, ba Talakawa ba ne kawai ta ke shafa, shima yana cikin firgici.
“Sha’anin tsaro ba na talaka ba ne kadai, ni ma ina cikin firgita, an dauki sarki a kasarnan,  an dauki soja, an dauki Dasanda, an dauki Dan siyasa, ni ma a cikin tsoro na ke. Sa bo da haka Allah dai ya kawo ma na sauki”.
Da ga karshe Majalisar Datttawa ta umarci Hafsoshin Tsaron da su kara kokari, mu ma za mu kara kokari na ganin cewa su na yin abun da ya kamata don kawo karshen matsalar tsaro a Kasarnan in ji Sanata Wadada.
Ganawar Majalisar Datttawa da dukkan Hafsoshin Tsaron Karsarnan da Mai bawa Shugaban Kasa Shawara akan Harkar Tsaro,  Nuhu Ribado da Ministocin Tsaro da na Kudi sun shafe kimanin awoyi goma su na ganawa don lalubo mafita akan matsalar tsaro da ta addabi kasarnan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here