Home Kwadago FCC: Na Rantse Da Alqur’ani Ba Ni Da Hannu Akan Badakalar Sayar...

FCC: Na Rantse Da Alqur’ani Ba Ni Da Hannu Akan Badakalar Sayar Da Offa – Dankaka

239
0
Dankaka

Shugaban Hukumar Kula da Daidaito Wajen Daukar Ma’aikata a Najeriya wato “ Federal Character Commission(FCC)” Hajia Muibat Farida Dankaka ta rantse da Alqur’ani Mai girma cewa ba ta da hannu wajen badakalar sayar da takardar aiki (Offa) da ake zargin Hukumar ta da yi .

Dankaka ta yi wannan ratsuwane a gaban Kwamitin Majalisar Wakilai mai bincike akan badakalar daukar aiki da ake zargin Hukumar da yi ranar Litinin a zauren taron Majalisar.

Ya yin da take Jawabi a gaban Kwamitin Hajia Dankaka ta ce Haruna Kolo wanda shine ake zargi akan gaba wajen sayar da Offa ga Yan Najeriya akan miliyoyin Nairori da ya ji tsoran Allah ya fadi gaskiya cewa ba ta da hannu akan wannan harkalla da ya gudanar.

“ Na rantse da Alqur’ani Mai girma ba ni da hannu akan badakalar daukar aiki da ake zargi na da shi kuma idan ina da hannun ko na taba karbar ko kobo da ga hannun Haruna Kolo Alqur’ani ya cini” Inji Farida Dankaka.

Hajia Dankaka wacce ta ke Magana cikin yanayi na mamaki na yadda Haruna Kola ya ke alakantata da wannan badakala ta kalubalance shi da ya bada hujja gamsassa da ke nuna tana da hannu a cikin wannan harka idan ya na da ita.

A na sa jawabin Haruna Kolo ya tabbatarwa da Kwamitin cewa ya karbi miliyoyin kudade da ga hannun jama’a da ga Naira Miliyan 1 zuwa Miliyan 2 amma duk wadannan kudade da ya karba bashi da sheda na banki  woto “ transfer” da ya ke tura kudin ga asusun Hajia Dankaka.

Kolo

Yayin da ya ke karin haske, Kolo ya ce kudin idan ya karba zunzurutunsu ya ke kai ma Hajiya Farida Dankaka gida; ikirarin wanda ta karyata cewa gidanta ba’a zuwa sai da izinin ta Kuma Jami’an tsaron ta na Farin Kaya sheda ne domin baccine kawai yake rabata da su tunda ta fara aiki da Hukumar.

Haruna Kolo ya tabbatarwa da Kwamitin cewa ya karbi wadannan kudade da ga hannun mutane kimanin mutum 25 da ga naira miliyan 1 zuwa miliyan 2 a kowannen su.

Shugaban Kwamitin Yusuf Gagdi ya sha alwashin yin adalci ga dukkannin wadanda ake zargi da badakalar sai dai ya ja hankalin su cewa tuni kwamitin sa ya yi bincike akan duk wadanda ake zargi da badakalar kuma suna da bayanai akan su sabo da hakan idan sun fadi karya ma, a karshe bincike gaskiya za ta yi halinta.

Yusuf Gagdi ya sanar da Haruna Kolo cewa Kwamitin ya na da bayanai na kudade da suka shiga asusun sa da kuma wadanda ya turawa kudi. Inda ya kara da cewa a asusun sa guda daya da ya ke da shi sun gano kudi kimanin Naira Miliyan 38.

A cikin asusun bankunan sa guda uku kuma sun gano jimillar kudi kimanin Naira Miliyan 75. Sabo da haka ya basu hadin kai ya fadi gaskiya ga Kwamiti kamar yadda ya yi alkawari a rantsuwar da ya yi.

Gagdi ya tambayi Kolo cewa a matsayin sa na Ma’aikace da ake biyan N110 a kowanne wata ta ya ya ya sami wadannan makuden kudade a asusun sa? Ya ce wadannan bayanai bincike ne kawai zai tantance gaskiyar al’umara.

Shugaba Gagdi ya kara da cewa dukkan Kwamishinonin da suke Hukumar da sauran ma’aikata da ake zargi su na da hannu ana da bayanai akan su kuma su na bibiya akan wadanda suke da alaka da su; sabo da haka a karshe bincike zai nuna masu gaskiya da marasa gaskiya.

Yusuf Gagdi ya umarci magatakardan Kwamitin da ya gaiyaci sauran mutane da ake zargi da su baiyana a gaban Kwamitin ranar Talata tare da shi Haruna Kola domin su cigaba da bawa Kwamitin bayanai da za su tantance gaskiyar al’amari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here