Home Tsaro Fargaba a Sokoto: Sakamakon Dauki-ɗai-ɗai da Yan bindiga

Fargaba a Sokoto: Sakamakon Dauki-ɗai-ɗai da Yan bindiga

184
0
Sokoto Governor

Wasu garuruwa a yankunan ƙananan hukumomin Gudu da Gwaranyo da ke jihar Sokoto a Najeriya na zaman ɗar-ɗar inda wasu ke ƙaura sakamakon yadda ƴan bindiga suka matsa musu.

Daga cikin mazauna yankin da lamarin ya shafa sun gaya wa BBC cewa ce da dama daga cikin al’ummarsu na hijira zuwa ƙananan hukumomin da ke maƙwabtaka da su, yayin da wasu ke ƙetarawa Jamhuriyar Nijar domin tsira da rayukansu.

Jama’ar sun ce ƴan bindigar na kai musu farmaki ba ƙaƙƙautawa saboda taɓarɓarewar tsaro inda a cikin kwanakin nan suka ce sun ɗauki wajen mako biyu suna kai musu hari a jere.

Daga cikin hare-haren da ɓarayin ke kai musu a baya-bayan nan sun ce an yi kwanaki suna kwashe musu mutane tare da hallaka wasu a sama da ƙauyuka shida.

Girman matsalar

Wani daga cikin mazauna yankin wanda a halin da ake ciki ya ce lamarin ya tilasta masa tserewa, kamar sauran mazauna, ba ya tare da iyalinsa ba ya tare da iyayensa.

“Akwai masu abinci (a gona) amma sun kasa yi saboda zaman fargaba,” in ji shi.

Ya ce ba daɗewa a cikin kwanakin nan ‘yan ta’adda sun shigar musu wasu ƙauyuka wajen uku, da hantsi inda suka tattara mutane suka tafi da su.

”Sun kashe mutum biyu a Giyawa sun kashe mutum biyu a Ɗanwaru,” a cewarsa.

Ya ƙara da cewa a sanadiyyar lamarin wasu daga cikin jama’ar yankin na tserewa zuwa ƙananan hukumomin da suka haɗa da Gwaranyo da Wurno.

Haka shi ma wani mazaunin yankin ƙaramar hukumar Gudu ya gaya wa BBC cewa a yanzu sun shafe kusan mako biyu ƴan bindigar na addabarsu kusan kullum.

Ya ce: “A yammacin Alhamis ɗin nan sun tare mana hanya, ranar Laraba sun tare mana hanya, ranar Talata sun tare mana hanya, Litinin sun tare mana hanya inda suke kwashe mana mutane a garuruwa da kauyuka daban-daban.”

Mutumin ya ce wannan halin da suke ciki ya sa wasu daga cikin jama’arsu ke tsallakawa zuwa yankin Jamhuriyar Nijar domin tsira da rayukansu.

Dangane da jami’an tsaro mutumin ya ce, su sun fi amfana da ƴan banga waɗanda ya ce su ne suke zuwa dare da rana su tsaya kan hanya domin tabbatar musu da tsaro.

“Kuma akwai sojoji da ƴan-sanda amma mu mafi a’ala ƴan-banga sun fi mana amfani bisa gare su,” in ji shi.

Me jami’ai ke cewa?

Kakakin rundunar ƴan-sanda ta jihar ta Sokoto ASP Ahmed Rufa’i, ya ce rundunarsu na da masaniya a kan labarin abubuwan da ke faruwa a wasu wuraren amma kuma wasu ba sa samun labari.

”Abubuwan da ke faruwa a wasu wuraren kamar na Gudu da Gwaranyo wanda aka yi jiya (Laraba),” ya ce.

Ya tabbatar da wani hari da ƴan bindigar suka shiga uankin inda ya ce sun samu wata mota da kaya har suka ƙone ta, amma ya ce ba su tafi da kowa ba.

“A Giyawa sun kashe mutum huɗu sun ɗauki mutum goma sha takwas amma bakwai sun samu sun tsira,” in ji shi.

Game da zargin rashin jami’an tsaro isassu, kakakin ya ce ba ko ina ne garuruwan suke kusa da Gwaranyo ba, saboda haka ba ko ina ne ake da ƴan-sanda ba.

Ya ce, ”amma duk da haka gwargwado ana yi, muna samun ƙari ta wurin sojoji da ƴan-banga.”

Matsalar masu satar mutane domin karɓar kuɗin fansa aba ce da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a wasu jihohi a Najeriya musamman na arewaci da suka haɗa da Sokoto da Zamfara da Kebbi da Naija, duk kuwa da matakan da hukumomi ke cewa suna ɗauka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here