Home Addini Farashin Aikin Hajji: Majalisar Wakilai Ta Bukaci Shugaba Tinubu Da Ya Saukakawa...

Farashin Aikin Hajji: Majalisar Wakilai Ta Bukaci Shugaba Tinubu Da Ya Saukakawa Yan Najeriya

93
0
Hon. Ajilo 3

Majalisar Wakilai ta bukaci Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu da ya  saukakawa Yan Najeriya a kan farashin da a ka saka na N5m  don gudanar da aikin Hajji a wannan shekara ta 2024 zuwa wani farashi da za su iya biya duba da matsi na tattalin arziki da ake ciki.

Majalisar ta bukaci wannan sauki ne bayan da Hon. Umar Ajilo da ga Jihar Kaduna ya gabatar da Kuduri a gaban Majalisar in da ya nemi Majalisar da ta nemawa Yan Najeriya sauki akan farashin da aka saka.

Ya ce aikin Hajji na da ga cikin rukunai biyar na addinin Musulunci wanda ya bukaci Musulmai ma su hali da su aiwatar da wannan Ibada a kalla sau daya a ruwar su amma ya ce farashin da aka saka ya yi yawa lura da irin halin da tattalin arzikin mafi yawan Yan Kasar su ke ciki.

Hon. Ajilo ya ce a halin yanzu abun da ya fi damun Yan Najeriya shi ne yunwa da abinci da za su ci amma duk da haka aikin Hajji Ibada ce da duk Musulmi ya na da bukatar ya aiwatar da wannan Ibada.

Ya ce a halin yanzu, mutanen da su ka iya biyan kudin aikin Hajjin ba su taka kara sun karya ba; wanda ya ce ada, gurbin da a ke warewa Yan Najeriya kadan ya ke yi musu amma a halin yanzu neman mutane a ke yi da za su cike gurbin.

Dan Majalisar ya ce  wannan dalili ne ya sa ya gabatar da wannan kuduri in da ya ne mi Majalisar da ta shiga tsakani ta hanyar gaiyatar Hukumar Aikin Hajji ta Kasa NAHCON da ta yiwa Majalisar bayani akan halin da ake ciki da yadda za a bi don saukakawa Yan Najeriya akan farashin da aka saka.

Ajilo ya kara da cewa, idan gwamnatin taraiya ta so zata iya saukakawa Yan Najeriya farashin aikin Hajjin domin Ibada ce  sau daya a shekara kuma idan ta so zata iya saukakawa Yan Kasar. Sabo da haka ya roki Shugaban Kasa Bola Tinubu da ya saukawa Yan Najeriya.

Da ga karshe Dan Majalisar ya yi kira ga Yan Najeriya da su taya su da addu’a wajen ganin wannan bukata da ya gabatar ta samu amincewar Shugaban Kasar don saukakawa Yan Najeriyan su sauke wannan farilla ta addinin Musulunci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here