Home Muhalli Falasɗinawa Fiye Da 300,000 Sun Rasa Matsuganansu A Zirin Gaza — MDD

Falasɗinawa Fiye Da 300,000 Sun Rasa Matsuganansu A Zirin Gaza — MDD

163
0
Ruguzau a Palasdin

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutane dubu dari 3 da 38 ne luguden wutar da Isra’ila ke ci gaba da yi a kan Gaza ya tilasta musu barin gidajensu.

A gefe guda kuma, mahukuntan yankin suka ce adadin wadanda suka mutu a bangarensu ya kai dubu 1 da dari 2.

A wata sanarwar Hukumar Kula da Ayyukan Jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce zuwa daren Laraba, adadin wadanda luguden wutar Isra’ila ya ɗaiɗaita a yankin Gaza ya karu da kimanin mutane dubu 75, daga wanda ta bayar tun da farko, inda a yanzu adadin ya kai dubu dari 3 da 38 da dari 9 da 34.

Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da Isra’ilar ke ci gaba da luguden wuta a kan wuraren da take ganin sansanonin mayakan kungiyar Hamas ne a yankin na Gaza, yankin da ke da yawan al’umma miliyan 2 da dubu dari 3, a matsayin martani ga hari mai ban mamaki da Hamas ta shammace ta da shi a ranar Asabar.

A bangare guda alkaluman wadanda suka mutu a yakin na Hamas da Isra’ila, bangaren yahudawa akwai mutane dubu 1 da 200 galibi fararen hula baya ga sojoji kusan 200 sai kuma a harin mafi muni da Isra’ilan yahudu ta taba fuskanta a tarihi.

A bangaren Gaza kuwa ma’aikatar lafiyar yankin ta ce adadin wadanda suka mutun ya kusa dubu 1 da 200 lura da yadda Sojin Isra’ila ke ci gaba da luguden wuta a lungu da sako na birnin. (Aminiya).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here