Home Ilimi Fadada Kudaden Shiga: Ilimantar Da Jama’a Harkar Kifi Zai Bunkasa Arzikin Yan...

Fadada Kudaden Shiga: Ilimantar Da Jama’a Harkar Kifi Zai Bunkasa Arzikin Yan Najeriya – Inji Sanata Wadada

109
0
Sanata Wadada Kifi

A wani mataki na  rage dogara da man fetur a matsayin hanya daya tilo na samar da kudaden shiga an nuna muhimmancin ilimantar da al’umma ga me da harkar Kifi a wani mataki na fadada hanyoyi na samar da kudaden shiga don bunkasa tattalin arzikin Yan Najeriya da ma Kasar baki daya.

Dan Majalisar Taraiya mai Wakiltar Nasarawa ta Yamma , Sanata Aliyu Ahmad Wadada ne ya nuna muhimmancin ilimantar da jama’ar game da harkar Kifi a matsayin wata hanya da zata fadada hanyoyin samun kudaden shiga ga Yan Kasa dama gwamnati baki daya.

In da ya ke Karin haske akan Kudurin da ya gabatar a zauren Majalisar Dattawa wanda tu ni ya shallake karatun na farko da na biyu ya ce dalilinsa na gabatar da Kudurin shi ne ya lura cewa Allah ya albarkaci kasarnan da Kifi da sauran halittun ruwa amma Yan Kasa kalilan ne su ke amfana da arzikin.

Ya ce daliln hankan shi ne rashin ilimi da mutane ba su da shi, shi ya sa ya gabatar da Kuduri domin a samar da Makarantu da za su rinka ilimantar da jama’a ilimin Kifi da sauran albarkatun ruwa a wani mataki na bunkasa tattalin arzikin su dama na Kasa baki daya.

Wadada ya kara da cewa abun takaici ne yadda wasu kasashen suke amfana da arzikin Kifin da Allah ya bawa Kasarnan amma Yan Najeriya ba sa amfana. In da ya kara haske akan yadda wasu kamfanonuwa na Kasashen waje su ke zuwa Tekun Kasarnan su debi Kifi mai yawa; su koma kasashen su, sannan su sarrafa shi su dawo mana da shi mu saya da tsada.

Sanata Wadada, ya ce bayan Teku, Najeriya tana da manyan fadamu da koguna a sassa daban-daban da suke Kasarnan harda ma Jihar sa ta Nasarawa da su ke da Kogin Benue da ya hadu da Kogin Neja in da za’a iya kiwon kifi na kasuwanci domin inganta tattalin arzikin Yan Najeriya.

Ko da ya ke ya ce Makarantar a Jihar sa ta Nasarawa ya ke so a fara kafa ta amma, burin sa shi ne a gina irin wadannan makarantu  a  dukkan sassan Najeriya domin aci albarkacin arzikin Kifi da Allah ya yiwa Kasarnan. Wanda ya ce idan an yi hakan, zai taimaka wajen samar da aiyukan yi da maganta zaman banza da dubbin matasan Kasarnan su ke fama da shi.

Wadada ya kara da cewa tun da Kudurin na sa ya shallake Karatu na biyu; yanzu abun da ya rage shine jin ra’ayin jama’a a wani mataki na tattara bayanai da za su taimaka wajen samar da makarantar wadda da zarar hakan ya tabbata za’a yiwa Dokar karatu na uku; wanda idan Majalisar Dattawa ta amince da ita Kudurin zai zama Doka da zarar Shugaban Kasa ya saka hannu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here