Home Siyasa Dan Takara Mai Zaman Kansa Zai Kawo Karshen Siyasar Ubangida A Najeriya...

Dan Takara Mai Zaman Kansa Zai Kawo Karshen Siyasar Ubangida A Najeriya – Inji Majalisar Dattawa

156
0

Majalisar Dattawa tace amincewa da sukayi da Kudurin da ya bawa Dan takara Mai Zaman Kansa wato Indipenda dama na ya tsayawa takara ba tare da jam’iya ba wata dama ce da za kawo karshen siyasar ubangida a  Najeriya.

 

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Abdullahi Gobir ne ya fadi haka a hirar sa da Yan jaridu a ofishin sa dake Abuja a jiya Talata.

 

Yace, wannan kudiri har ila yau zai kawo karshen kakabawa mutane dan takara da jam’iyu suke yi ba tare da la’akari da chanchanta ko rashin chanchantar dan takarar ba.

 

Sanata Gobir ya kara da cewa, sun amince da wannan kuduri ne sakamakon goyon baya da kudurin ya samu na kananan hukumomin kasarnan guda 27 daga cikin 36.

 

“Wannan kuduri na jama’a ne domin kuwa ya sami amincewar kananan hukumomi 27 daga cikin 36. Mu kuma duk abin da jama’a suke so shi zamuyi”

 

Sanata Gobir yace,  yanzu abin da ya rage shine Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya saka hannu akan kudurin domin ya zamo doka.

 

“Kuma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai amince da wannan kuduri domin shi a ko da yaushe yana duba ne akan abun da jama’a suke so. Sabo da haka zai saka hannu da zarar yaje gaban sa.”

 

Sanata Gobir ya cigaba da cewa wannan kuduri zai bawa wadanda jama’a suke so dama na su tsaya takara kuma su sami nasara ba tare da wata matsala ba muddin jama’a sun amince da hakan.

 

Sai dai yace, masu hali ma sun sami dama na tsayawa takara domin kuwa ita siyasa ta na bukatar kudi wadanda hukumar zabe take sawa duk mai sha’awar tsayawa takara a jam’iyance ko kuma a dai dai ku.

 

Shugaban Masu Rijayen na Majalisar Dattawa ya ce wannan ba karamin cigaba ne aka samu ba a siyarsar Najeria kuma hakan zai kawo cigaba kamar yadda ya kawo a kasar Amurka inda wasu kan tsaya takara a Indipenda kuma su ci nasara musamman a Majlisar Dattawa da Wakilai dama Kananan hukumomi a Amurka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here