Home Siyasa Dalilin Da Abba Gida-Gida Bai Je Muhawarar ’Yan Takara Gwamann Kano Ba

Dalilin Da Abba Gida-Gida Bai Je Muhawarar ’Yan Takara Gwamann Kano Ba

223
0

Dan takarar gwamnan Jihar Kano a Jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf bai halarci taron muhawarar ’yan takarar gwamnan jihar ba da aka gudanar a ranar Asabar.

Dan takarar da aka fi sani da Abba Gida-gida ya ce bai halarci muhawarar da kamfanin Media Trust masu jaridun Daily Trust da Aminiya da tashoshin Trust TV da Trust Radio ya shirya ba ne saboda wasu dalilai da suka fi karfinsa.

Daraktan kwamitin yakin neman zabensa, Hisham Habib, ya sanar a safiyar Asabar cewa, Abba Gida-Gida, “ya so halarta, amma abun takaici, wani al’amari da ya taso masa ya sa ba zai samu zuwa ba,” Habib.

Wanda ya jagoranci muhawarar kuma shugaban kwamitin tsare-tsare, Dokta Suleiman Suleiman, ya sanar a lokacin taron cewa dan takarar ya aiko da sakon ban hakuri cewa zai halarci wani muhimmin taro a kasar waje.

Wadanda suka halarci taron sun hada da na PDP, Muhammad Sani Abacha, da na Jam’iyyar LP, Bashir I Bashir da Nasiru Yusuf Gawuna na APC.

An gudanar da taron ne a Jami’ar Bayero ta Kano, kuma na yada shi a kafofin Media Trust da suka had da Daily Trust, Aminiya and Trust TV.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here