Home Kotu da 'Yan sanda Dalilan Mu Na Rushe Masarautar Kano – inji Hon....

Dalilan Mu Na Rushe Masarautar Kano – inji Hon. Dala

291
0
IMG 20240523 WA0069

 Majalisar dokoki ta jihar  Kano a arewacin Najeriya ta amince da rushe duka masarautun jihar bayan soke sabuwar dokar da ta ƙirƙiri sababbin masarautu a 2019.

Hakan na nufin cewa an koma amfani da tsohuwar dokar da ta kafa masarautar Kano.

Majalisar ta ɗauki matakin ne a zaman da ta yi ranar Alhamis.

Sabon matakin da majalisar ta ɗauka ya nuna cewar sarakunan jihar biyar na Kano, da Bichi, da Ƙaraye, da Gaya, da Rano duk sun rasa kujerunsu

Idan har Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu a kan sabuwar dokar hakan zai ba shi damar naɗa sabon sarki a masarautar Kano.

“Wannan doka ta bai wa gwamna iko, tun da an dawo da masarauta guda ɗaya, ya tuntuɓi masu zaɓen sarki su ba shi sunan wanda zai zama sarkin Kano,” kamar yadda Shugaban Masu Rinjaye na majalisar Kano Lawan Hussaini Dala ya yi bayani

“Yanzu babu sarki ko ɗaya a Kano,” in ji shi.

‘Yan majalisar kuma sun gabatar da sabuwar dokar da za ta ƙirƙiri sabbin sarakuna masu daraja ta biyu.

“A gobe [Juma’a] za mu yi wa dokar kafa masarautu masu daraja ta biyu karatun farko insha Allahu,” a cewarsa.(BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here