Home Wutar Lantarki Dalilan Majalisar Dattawa Na Kafa Kwamiti Don Bincikar Tarnakin Da Ya Hana...

Dalilan Majalisar Dattawa Na Kafa Kwamiti Don Bincikar Tarnakin Da Ya Hana Samar Da Wutar Lantarki A Mambila

123
0
Mambilla power project site

Majalisar Dattawa ta kafa wani Kwamiti na wacin gadi mai karfi domin bincikar dalilai da su ka yiwa masamar Wutar Lantarki ta Mambila tarnaki tun da ga shekara ta 1999 kawo yanzu a wani mataki na ganin an samar da Karin hasken wutar lantarki a Kasarnan.

Majalisar ta dauki wannan mataki ne biyo bayan wani Kuduri na gaggawa da Dan Majalisar Taraiya mai Wakiltar Jihar Taraba ta Tsakiya, Sanata Haruna Manu ya gabatar tare da hadin gwiwa da ga Sanatoci sama da 40 a zauren ta ranar Alhamis.

Kwangilar aikin wacce a ka bawa wasu Kamfanonin China guda uku wadan da su ka hada da CGGC da SHC da CGOC a shekara ta 2017 a kan kudi Dalar Amurka Biliyan 5.792 domin samar da wutar lantarki mai karfin haske 3,050.

Gwabnatin Tshohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ce ta bayar da aikin a kan wata yarjejeniya da Kasar China wacce za ta samar da kaso 85 na kudin da za’a yi aikin; ita kuma Najeriya za ta samar da kaso 15 wanda za a gama aikin a cikin watanni 72.

Lura da muhimmancin wannan aiki, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya kafa wani Kwamiti don ganin wannan aikin samar da wutar Lantarki ya zamo gaskiya sabo da zai tallafawa wannan kasar wajen samar da wutar lantarki mai dorewa da zata farfado da kamfanin Ajaokuta da sauran kamfanoni a Kasarnan.

Tinubu ya ce idan a ka samar da wannan wutar za ta tallafawa Kasarnan wajen farfado da arzikin Najeriya a fannoni da dama. Ku ma zai samawa Yan Najeriya mutum 55,000 aikin yi; da kuma mutum 100,000 gidaje domin gusar da mutane da su ke kusa da gurin. Har ila yau, zai bunkasa tattalin arzikin yan Kawangila da Yan Kasuwra Kasarnan.

Hakan ta sa a ka samar da wani tsari da zai bawa Yan Najeriya dama su ma su amfana da ga  Kwangilar ta hanyar samar da hukumomi da za su saka ido akan aikin.

Hukumomin sun hada da ta Wutar Lantarki da Ruwa da Tsaftar Muhalli da Kudi da Tsare-tsare da kuma ta Kasafin Kudi da ta Shari’a don saka ido don ganain aikin ya tafi ba tare da wata matsala ba.

Dadin da dawa, hukumomin gwamnatin Taraiya guda 27 ne da kuma kamfanonin Yan Kasuwa ma su zaman kan su guda 500 ne za su ci gajiyar kaso 15 na wannan aikin na Gwamnatin Taraiya.

Sen. Manu Taraba Central

Wannan aikin ya samu sahalewar Doka ta 5 da ke da karfin fadar Shugaban Kasa don ganin aikin ya tafi ba tare da wata matsala ba wajen bawa Yan Najeriya dama su ci gajiyar aikin ta hanyar samar da kayan aikin da ga cikin gida Najeriya.

Da ya ke Karin haske a kan Kudurin, Sanata Haruna Manu ya ce dalilin sa na gabatar da Kudurin a wannan lokaci shi ne ganin irin muhimmanci da aikin ya ke da shi amma shekara da shekaru an kasa aiwatar da shi.

Bayan haka ya kara da cewa, a matsayin sa na dan Majalisa da ga wannan yanki na Arewa maso Gabas; samar da wannan aikin zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin yankin da ma Najeriya baki daya ganin yadda wutar Lantarki ta ke da tasiri ga wannan zamani da ya dogara da na’urorin zamani.

Sanata Manu ya yabawa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu da ya dauki wannan aiki da muhimmanci ganin yadda ya saka shi da ga cikin aiyukan da zai yi a gwamnatin sa a wani mataki na dawo da martabar Kasarnan a cikin gida da ma duniya baki daya.

Kudurin ya samu karbuwa a zauren Majalisar, a yayin da sanatoci da dama su ka bayar da gudunmawar su wajen nuna muhimmanci aikin ga Najeriya ta fannin bunkasa masana’antu da kimiyyar zamani da kasuwanci da ma zaman takewa baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here