Home Siyasa Dalilan INEC na dakatar da tattara sakamakon zaɓen gwamna a Adamawa

Dalilan INEC na dakatar da tattara sakamakon zaɓen gwamna a Adamawa

249
0

Hukumar zaɓen Najeriya mai zaman kanta INEC ta bayyana dakatar da aikin tattara sakamakon zaɓen gwamna a jihar Adamawa.

Cikin wata sanarwa da babban jami’inta kan yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe na ƙasa, Barrista Festus Okoye ya fitar, INEC ta ce matakin da kwamishinan zaɓe na jihar Adamawa – REC ya ɗauka na sanar da wanda ya lashe zaɓe haramtacce ne, don haka ta ce ba za a yi amfani da shi ba.

Sanarwar ta ce kawo yanzu ba a kammala tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Adamawa ba.

Hukumar INEC ta gayyaci duka jami’anta da ke lura da zaben gwamna a jihar Adamawa, su kama hanyar zuwa Abuja domin yin wani taron gaggawa.

Hukumar INEC ta gudanar da cikon zaɓen gwamnan jihar Adamawa ne a ranar Asabar 15 ga watan Afrilu, bayan ta ayyana zaben da aka yi a makonnin da suka wuce a matsayin wanda bai kammala ba.

Gwamna Ahmadu Umar Fintiri na jam’iyyar PDP shi ne ke kan gaba bisa alkaluman da hukumar INEC ta sanar kawo yanzu, yayin da Aishatu Dahiru Binani ta jam’iyyar APC take bi masa a yawan ƙuri’u.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here