Home Kotu da 'Yan sanda Dalilan ICPC Na Tsare Mawaki D’Banj

Dalilan ICPC Na Tsare Mawaki D’Banj

208
0

A ranar 8 ga watan Yunin 2016 gwamnatin Muhammadu Buhari ta kirkiro shirin na N-Power don tallafawa matasa da ba su da aikin yi.

Hukumar ICPC da ke yaki da cin hanci da sauran ayyukan almundahana a Najeriya, ta ce ta tsare mawakin Afrobeat Mr. Oladipo Daniel Oyebanjo, wanda aka fi sani da D’Banj.

ICPC ta ce tsare ta mawakin ne bisa binciken kan wasu kudade na shirin N-Power da gwamnati ta kirkiro.

A ranar 8 ga watan Yunin 2016 gwamnatin Muhammadu Buhari ta kirkiro shirin don tallafawa matasa da ba su da aikin yi.

“Mun karbi korafe-korafe kan yadda aka karkata akalar kudaden N-Power da yawansu ya kai biliyoyin naira, bayan da gwamnatin tarayya ta amince a fitar da su don tallafawa mutane.

“Da yawa daga cikin mutanen da ya kamata su amfana da kudin, sun yi korafi kan rashin karbar kudaden wadanda ake bayarwa a duk wata, duk da cewa gwamnati ta fitar da su.” Sanarwar da ICPC ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce.

Hukumar ta ce ta gayyaci akalla mutum 10 cikin watannin da suka gabata, wadanda suke da alaka da almundahanar kudaden na N-Power, tana mai cewa an ba da belinsu bayan da aka tsare su.

A cewar ICPC, a baya ta sha turawa D’Banj takardar gayyata don ya bayyana a gaban masu bincike, amma abin ya ci tura. (VOA)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here