Home Siyasa Dalilan Da Su Ka Sa Majalisar Dattawa Ta Mai Da Hukumar Bada...

Dalilan Da Su Ka Sa Majalisar Dattawa Ta Mai Da Hukumar Bada Tallafi Karkashin Shugaban Kasa – Munguno

221
0
Sen. Munguno

Majalisar Dattawa ta ce dalilan da su ka sa ka ta mayar da Hukumar Tallafi karkshin kulawa Shugaban Kasa shi ne sabo da su tabbatar da cewa duk wani tallafi da za a bayar ya kai ga wadanda su ke bukata ba tare da wani shamaki ba.

Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Borno ta Arewa Sanata, Muhammad Tahir Munguno ne ya sanar da haka a wata hirar sa da Yan Jaridu ranar Juma’a a ofishin sa da ke Majalisar Taraiya Abuja.

Ya ce sun lura cewa a gwamnatin da ta shude sun lura cewa an yi wakaci ka ta shi wajen rabawa Yan Najeriya tallafi sa bo da haka ne su ka ga zai fi dacewa su mayar da Hukumar karkashin kulawar Shugaban Kasa tun da shine uban kowa kuma tsarin shi ne ya fito da shi domin al’umar Najeriya.

“Shugaban Kasa shi ya fi cancanta na ya shugabanci wannan Hukumar a matsayin sa na uban kasa kuma shi Yan Najeriya su ka zaba. Sabo da haka mu na ganin idan shi ke kula ta tsarin, tsarin zai fi samun kulawar da ta kamata. Domin ba zai yarda wani ya yi abun da bai kamata ba, wanda hakan zai bata masa suna”.

Bayan haka, Sanata Munguno ya ce a baya Hukumar ba ta da wata Doka da ta ke gudanar da ita amma, yanzu mun yi Doka wadda ta tanadi tsare-tsare da hukunce-hukunce da za su tafiyar da ita.

“kafin wannan lokaci Hukumar ba ta da wata Doka da ta ke yi mata jagora. Minista ko kuma wanda aka nada shi ne ya ke da wuka da nama na raba tallafin yadda ya ga dama. Amma a yanzu akwai dokoki da za su yi wa Hukumar jagoranci”.

Sanata Munguno ya ce ko da ya ke ba Shugaban kasa ba ne da kansa zai gudanar da Hukumar zai iya kafa wani kwamiti karkashin kulawar sa domin ya tabbatar da cewa an aiwatar da tallafin kamar yadda ya kamata.

Ya ce aikin Hukumar shine ta bayar da tallafin ga mutane marasa galihu a Najeriya sabo da haka sun fito da tsare–tsare da yadda za a zakulo irin wadannan mutane domin tallafin ya kai gare su. Da ga cikin tsarin shi ne samar da wani kundi da ke dauke da sunaye da bayanai na marasa galihu a kananan hukumomi 774 da unguwanni da ke Najeriya.

Sanatan ya kara da cewa, tsarin ba ya bukatar sanin matakin ilimin wadanda za bawa tallafi, abu mafi muhimmanci shi ne shin ka cancanci tallafin kuma kai dan Najeriya ne? kuma a ina ka ke da zama kuma ta ya ya za a sadar da tallafin gare ka musam asusun banki.

Da ga karshe Sanata Munguno ya ce bayan haka sun tanadi hukunce hukunce na Doka domin ladabtar da duk wanda ya karya daya da ga cikin Dokoki da su ka tanada na gudanar da Hukumar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here