Home Uncategorized Dalilan da ke janyo rikici tsakanin ƴan siyasa da sarakai a Najeriya

Dalilan da ke janyo rikici tsakanin ƴan siyasa da sarakai a Najeriya

70
0
Sarakai 3

Yunƙurin yi wa dokar masarautu gyaran fuska a jihar Sokoto da takardar tuhumar neman bahasi kan ƙin shirya hawan daba da gwamnatin jihar Katsina ta aike wa Sarkin na Katsina da kuma ɗauki-ba-ɗaɗi da ake yi tsakanin ɓangaren Muhammadu Sanusi II da Alhaji Aminu Ado Bayero a kan wane ne Sarkin Kano, na ci gaba da sanya tsoro a zuciyar ‘yan arewacin Najeriya kan makomar masarautun gargajiya a yankin.

Ana dai yi wa wannan al’amari kallon zaman tankiya tsakanin sarakan gargajiya da ƴan siyasa masu mulki.Kuma wannan ne ke sanya al’umma tambayar ko mene ne ke haddasa rikici tsakanin ɓangarorin guda biyu?

BBC ta tuntubu Farfesa Shu’aibu Shehu Aliyu, darekta na Cibiyar Bincike da Adana kayan Tarihi ta Arewa House da ke Kaduna da Dakta Raliya Zubairu Mahmud ta sashen nazarin tarihi a kwalejin Kumbotso Campus da ke Kano.

Masanan sun zayyana wasu dalilai guda uku da suka ce su ne ke janyo rashin fahimtar juna tsakanin sarakai da ƴan siyasa kamar haka

1) Rashin fayyace aikin sarakai a tsarin mulki

Tun farko dai babbar matsalar da ke sabbaba rikici tsakanin sarakunan gargajiya da ƴan siyasa ita ce rashin fayyace rawar da sarakunan ya kamata su taka a kundin tsarin mulkin Najeriya.

“Idan ka duba tsarin mulkin Najeriya ba a fayyace rawar da sarakan ya kamata su taka ba. Rashin sanin ayyukansu ne ya sa suke shiga abubuwan da ake ganin bai shafe su ba. Ko a gyaran fuskar da aka yi wa tsarin mulkin Najeriya na 1999, ba wani fayyacaccen tsarin da aka fitar musu.

Amma duk da rashin fayyacewar da tsarin mulkin bai yi ba, za ka ga har yanzu akwai abubuwan da ba a yi sai da su. Misali idan kana son sayen ƙasa sai da sa-hannun dagaci ko mai unguwa. Haka ma batun kasancewar mutum ɗan gari, dole sai da sa-hannun dagaci ko mai unguwa. Amma kuma duk ba sa cikin tsarin mulki. To me ya sa ba za a gyara a ba domin ba su waɗannan damarmakin ba.” In ji Dakta Raliya Zubairu Ahmad, ta sashen nazarin tarihi a kwalejin Kumbotso Campus da ke Kano.

2) Shigar sarakai siyasa

Zarge-zargen shigar sarakai siyasa kusan za a iya cewa na daga cikin manyan dalilan da ke ƙara rura wutar rikici tsakanin sarakunan gargajiya da ƴan siyasa.

“Sarki ya kamata ya zama uban kowa don haka bai kamata ya sa hannu a cikin siyasa ba. Kuma tsoma baki a siyasar ke janyo musu rashin ƙima a hannun ƴan siyasa. Kamata ya yi sarki ya zama mai saka ido mai kuma bayar da shawara.

Hakan zai sa ƴan siyasa su girmama shi. Amma idan ɗan siyasa ya fuskanci cewa sarki ko hakimi ko dagaci ko kuma mai unguwa ya nuna masa hamayya to idan ya samu dama ba zai bar shi ba. Ko dai ya tsige shi ya musanya shi da wani ko kuma ya bujuro da tsare-tsaren da za su rage masa ƙarfi.” In ji dakta Raliya.

3) Ƴan siyasa na ‘ƙullatar’ sarakai

Wataƙila mutanen da suka ci zaɓe kan ƙullaci sarakan gargajiya da suka tarar a kan mulki inda suke ɗaukar matakan wulaƙanta su sakamakon fahimtar cewa sarkin ya ƙalubalance su ko kuma ya nemarwa abokin hamayyarsu ƙuri’a.

“Wani lokacin ma za ka ga ƴan siyasar na da alaƙa da gidajen sarauta ko kuma su ma sun gaji sarautar. Ka ga kenan kujerun mulkin suna ba su damar ɗaukar fansa a kan sarakunan gargajiya ta yadda ko dai su cusa danginsu a tsarin sarautar ko kuma su cire sarkin da suka tarar domin dora jininsu ko abokansu.

Sannan a kan samu yanayin da wasu ƴan siyasa kan ƙullaci masarautar watakila saboda wani rikici da ya haɗa masarautar da mahaifansu ko kuma wani abu mai kama da haka. Wasu kuma kawai jininsu ne bai haɗu da sarakai ba bisa tunanin cewa sarakan ba su da wani muhimmanci a tsarin da ake ciki…” In ji dakta Raliya.

Lokacin da aka fara karya lagon sarakan gargajiya

Farfesa Shu’aibu Shehu Aliyu, darekta na Cibiyar Bincike da Adana kayan Tarihi ta Arewa House da ke Kaduna ya ce tun bayan cire sarakuna da dama da gwamna Lord Lugard ya yi a arewacin Najeriya, babban dalilin da ya fara janyo ƴan siyasa su raina sarakan gargajiya shi ne lokacin da aka fara siyasa a Najeriya a 1952, inda aka zaɓi wakilai daga lardunan uku na Najeriya.

“To a wannan lokaci an samu saɓani tsakanin mutanen da aka zaɓa suka zama ƴan majalisa daga lardin arewa da sarakan yankunansu. Misali an zaɓi mutum ya zama minista kuma idan ya koma garinsu zai shiga fadar sarki da takalmi sannan ya gaisa da sarki.

Wannan ne ya fara janyo rikici tsakanin ƴan siyasa da masarautu. Duk da dai daga baya an sauya cewa dole ne kowa idan ya koma gida ya yi biyayya ga al’adun gargajiya.

A baya kafin juyin mulkin farko, akwai majalisar sarakuna sannan sarakuna na cikin harkokin gwamnati inda wasu sarakunan ma suka zama ministoci kamar sarkin Kano Muhammadu Sanusi I ya taɓa zama gwamnan riƙon ƙwarya. Sannan sarkin Zazzau Jafaru ya taɓa zama minista. Haka ma sarkin Katsina Usman Nagwaggo ya taɓa zama minista”. In ji farfesa Shu’aibu Shehu Aliyu.

Farfesa Shu’aibu ya ƙara da cewa an fara karya lagon sarakan gargajiyar ne a shekarar 1966.

“To amma bayan juyin mulki musamman lokacin da aka yi gyaran tsarin mulki da ya samar da ƙananan hukumomi a 1966 sai aka fara cire wasu iko da sarakan gargajiya ke da su misali ‘yan doka da kotuna duk aka cire su daga hannun sarakuna.”

Haka aka yi ta yi har karshe lokacin da aka yi wa dokar ƙananan hukumomi kwaskwarima a 1988 wanda aka cire hannun sarakuna daga hannun mulki aka bar su tsurarsu”.

Abin da ya fi takaici ma shi ne yadda aka mayar da su ƙarƙashin ’yan siyasa misali hakimi na ƙarƙashin shugaban ƙaramar hukuma. Ko tafiya zai yi sai da izini. Hatta albashinsu na hannu ƙananan hukumomi”. kamar yadda farfesa ya ƙara haske.

Illolin wulaƙanta masarautun gargajiya

Farfesa Shu’aibu Shehu Aliyu ya danganta matsalolin da arewacin Najeriya ke fuskanta na rashin tsaro da shaye-shaye da irin yadda aka mayar da sarkan gargajiya koma-baya.

“A baya sarakan nan su ne shugabannin addini. Jama’a na martaba su sosai. Su ne hanyar da ake bi wajen isar da sako ga talakawa. Idan ka duba tun daga sarki, hakimi, dagaci har zuwa mai unguwa. Saboda haka lalata tsarin da aka yi na ɗaya daga cikin dalilan matsalar rashin tsaro a arewa. Saboda a baya duk wani baƙo idan ya zo gari gidan mai unguwa za a kai shi.”

Su kansu ‘yan siyasa na amfani da sarakunan ne wajen kai wa ga talakawa musamman idan ka dubi batun rijistar zaɓe, allurar rigakafi da dai sauransu. Duk da sarakunan gargajiya ake amfani. Saboda lalata wannan tsari ba ƙaramar illa ke yi wa tsarin zamantakewa ba a arewacin Najeriya.” In ji farfesa.

Mafita

Duka masanan guda biyu farfesa Shu’aibu Shehu Aliyu, darekta na Cibiyar Bincike da Adana kayan Tarihi ta Arewa House da ke Kaduna da Dakta Raliya Zubairu Mahmud ta sashen nazarin tarihi a kwalejin Kumbotso Campus da ke Kano, sun amince cewa fayyace ayyukan sarakunan gargajiya a kundin tsarin mulkin kasa ne kawai zai magance matsalar nan.

“Ya rage ga Najeriya ta fayyace irin rawar da sarakan nan za su taka a cikin al’umma domin har yanzu babu kamar su. Ka da a manta fa ko da lokacin mulkin Turawan mulkin mallaka ta hanyarsu ne turawan suka iya yin mulkin da suke so saboda muhimmancinsu.” In ji farfesa Shu’aibu.

To sai dai dakta Raliya ta ce matsalar da za a fuskanta koda an fayyace matsayin sarakan gargajiya a tsarin ƙasar ita ce “ai ƴan siyasar ne dai za su zauna su rubuta abin da suke so. Ka ga kenan jiya wa yau.”

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here