Home Cinikaiyar Zamani Dalilan CBN na ƙara wa’adin daina karɓar tsofaffin kuɗi

Dalilan CBN na ƙara wa’adin daina karɓar tsofaffin kuɗi

240
0

Babban Bankin Najeriya CBN ya sanar da ƙara wa’adin daina karɓar tsofaffin takardun kuɗi zuwa 10 ga watan Fabirairu.

Gwamnan Babban Bankin Godwin Emefiele ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

Gwamnan ya ce ya zuwa yanzu CBN ya karɓi naira tiriliyan ɗaya da biliyan 900 na tsoffin takardun kuɗi, inda kuma ya ce saura naira biliyan 900 ya kammala karɓar tsoffin takardun kuɗaɗen.

Ya yi bayanin cewa sai da CBN ya nemi sahalewar Shugaba Muhammadu Buhari domin ɗage wa’adin karɓar tsofaffin takardun kuɗin, wanda kuma ya amince a ƙara wa’adin da kwana 10.

“Sakamakon halin da ake ciki, mun nemi umarni kuma mun samu daga shugaban ƙasa kamar haka: ƙarin kwanki 10 na karɓar tsofaffin takardun kuɗi daga 31 ga watan Janairu zuwa 10 ga watan gobe na Fabrairu, za a ci gaba da karɓar kuɗin daga hannun ‘yan Najeriya a hukumance,” in ji sanarwar.

“Dama ta kwana bakwai, daga 10 zuwa 17 ga watan Fabrairu, domin al’umma su iya mayar da tsoffin kuɗadensu Babban Bankin Najeriya bayan cikar wa’adi, kamar yadda doka ta 20(3) da ta 22 ta Babban Bankin ta tanada”.

“Bayanan da muka samu tun daga 2015, sun nuna kuɗaɗen da ke yawo a hannun ‘yan Najeriya sun kai naira tiriliyan ɗaya da biliyan 400. Amma ya zuwa watan Oktoban 2022, alƙaluma sun nuna cewa akwai sama da tiriliyan uku da biliyan 230 da ke yawo a hannu mutane.

“Wannan na nuna cewa naira biliyan 500 ne kacal a hannun bankuna, yayin da naira tiriliyan biyu da biliyan 700 ke ɓoye a hannun wasu ƙalilan.”

Gwamnan CBN ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su zama masu biyayya da haɗin kai wajen tabbatar an gama mayar da kuɗaɗen ba tare da wani tashin hankali ba.

Gabanin wannan mataki dai, da dama daga cikin ‘yan Najeriya sun fuskanci yanayi maras daɗi wajen mayar da tsofaffin kuɗaɗensu zuwa bankuna.

Cikin sanarwar gwamnan Babban Bankin ya yaba wa Shugaba Buhari na haɗin kai da ya bai wa CBN domin gabatar da wannan sauyin kuɗin wanda ya ce “ya kamata a riƙa yi duk shekara biyar zuwa takwas, amma Najeriya yanzu ta shafe shekara 19 ba ta sauya nata kuɗaɗen ba”.

Manyan ‘yan siyasa a Najeriya irin su Atiku Abubakar da Rabi’u Musa Kwankwaso da Peter Obi da Bola Ahmed Tinubu sun yi kira ga CBN ɗin da ya ƙara wa’adin karɓar tsoffin takardun kuɗin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here