Home Cinikaiyar Zamani Daina Karbar Tsofaffin Kudi: Bankin IMF Ya Bawa CBN Shawarwari

Daina Karbar Tsofaffin Kudi: Bankin IMF Ya Bawa CBN Shawarwari

250
0

Asusun Ba Da Lamuni na Duniya (IMF), ya bukaci Babban Bankin Najeriya (CBN), da ya duba yiwuwar kara wa’adin daina karbar tsofaffin takardun kudi daga ranar 10 ga watan Fabrairu.

Asusun a cikin wata sanarwa a ranar Laraba ya ba da misalin yadda aka samu tabarbarewar kasuwanci da kuma tattalin arziki sakamakon canjin kudi.

“Bisa la’akari da wahalhalun da canjin kudi ya kawo da kuma cikas ga kasuwanci da kuma biyan kudade sakamakon karancin sabbin takardun kudi da jama’a ke fuskanta, duk da matakan da CBN ya bullo da shi na magance kalubalen da ake fuskanta game da canjin takardun kudi, IMF na bukatar CBN ya duba yiwuwar kara wa’adin daga ranar 10 ga watan Fabrairu,” in ji IMF.

Sanarwar ta fito ne daga hannun Laraba S. Bonnet, Manajar Ofishin Wakilin Mazauna Najeriya a madadinsa.

Bayanin na zuwa ne bayan da kotun koli ta hana CBN kin kara wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu.

Kotun ta bayar da umarnin ne a wani hukunci da ta yanke kan karar da gwamnatocin Jihohi uku suka shigar a gabanta.

Tun da farko dai CBN ya kayyade wa’adin zuwa ranar 31 ga watan Janairu amma ya kara wa’adin sakamakon matsin lamba daga ‘yan Najeriya. (Aminiya).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here