Home Diplomasiyya Daga Taron G20 A Indiya, ShugabaTinubu ya wuce Dubai

Daga Taron G20 A Indiya, ShugabaTinubu ya wuce Dubai

163
0
Tinubu in India

Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmad Tinubu zai ya da zango a Dubai daga taron G-20 da yake halarta a Indiya, domin ganawa da jagororin ƙasar.

Cikin wata sanarwa da fadar shugaban na Najeriya ta sanar wadda mai Magana da yawun Shugaban Kasar ya sanyawa hannu, Chief Ajuri Ngelale ta ce ganawar ci gaba ne na tataunawar jakadan ƙasar Haɗaɗdiyar Daular Larabawa ya yi da shugaba Tinubu a fadarsa da ke Abuja, domin magance wasu matsaloli na tsamin dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.

Sanarwar ta kuma ce shugaba Tinubu zai yi ƙoƙarin magance tsamin dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.

Shugaba Tinub ya halarci taron ƙungiyar G-20, ta ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki na duniya bisa gayyatar firaministan Indiya, wanda ya jagoranci taron.

Shugaban zai koma Najeriya da zarar ya kammala ganawa da jigogin na UAE, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here